'Ya tawayen Syria sun ƙwace babban birnin Damascus amma ba a san inda Shugaba Bashar al-Assad yake ba, a yayin da rahotanni ke cewa ya shiga jirgin sama ya tsere daga Damascus zuwa birnin Homs.
A yayin da 'yan tawayen suka karɓe babban birnin, wasu rahotanni a shafukan sada zumunta na intanet na cewa Assad ya arce bayan gwamnatinsa ta rushe.
Wasu shafukan intanet da ke bin diddigin tashi da saukar jiragen sama sun ce wani jirgi ya tashi daga filin jiragen saman Damascus kuma daga bisani an hango shi ya nufi birnin Homs ko da yake daga nan ba a ƙara jin ɗuriyarsa ba.
Wasu rahotanni da aka wallafa a shafin X sun ce jirgin yana ɗauke da Assad.
Kazalika akwai rahotannin da ke cewa jirgin ya yi ƙasa-ƙasa zuwa ƙafa 1,600 kafin a daina jin ɗuriyarsa kuma an ce an ji yana "wata tafiya da ba a saba gani ba."
Wakilin TRT World ya ruwaito cewa Assad ya tsere zuwa Iran ko Rasha bayan 'yan tawaye sun ƙwace Damascus.
'Yan tawaye sun shiga tsakiyar birnin Damascus ranar Lahadi bayan gwamnatin Assda ta kasa kare kanta. Daga bisani sun isa fadar shugaban ƙasa.