Katz (Dama) ya fitar da sanarwar ce jim kaɗan bayan Khamenei (Hagu) ya yi jawabi ga dandazon jama'ar da suka halarci sallar idi a Tehran, inda ya ce "gwamnatin shaiɗanu ta yi kuskure kuma dole a hukunta ta." / Hoto: AP

An yi ta ka-ce-na-ce tsakanin Isra'ila da Iran bayan mahukunta a Tehran sun yi alƙawashin yin ramuwar gayya sakamakon harin da Isra'ila ta kai a ofishin jakadancinsu da ke birnin Damascus na Syria, yayin da hukumomi a Tel Aviv suka sha alwashin yin raddi.

Hayaniyar da ta kaure tsakanin Isra'ila da Iran ta yi ƙarami ranar Laraba, inda Ministan Harkokin Wajen Isra'ila Katz ya wallafa wani gargaɗi ga Iran a shafukan sada zumunta.

A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, da harshen Hebrew da Persia wanda kai-tsaye ya tura wa Shugaban Addinin Iran Ali Khamenei, Ministan Harkokin Wajen Isra'ila Katz ya yi barazanar yin martani idan Iran ta kai hari a Isra'ila.

"Idan Iran ta kai hari a cikin ƙasarmu, Isra'ila za ta mayar da martani ta hanyar kai wa Iran hari," in ji shi.

Katz ya fitar da sanarwar ce jim kaɗan bayan Khamenei ya yi jawabi ga dandazon jama'ar da suka halarci sallar idi a Tehran, inda ya ce "gwamnatin shaiɗanu ta yi kuskure kuma dole a hukunta ta."

Khamenei na bayani ne game da zargin da ake yi wa Isra'ila da hannu a harin da aka kai wa ƙaramin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus ranar 1 ga watan Afrilu.

Isra'ila ta kashe manyan jami'an sojin Iran a harin da ta kai ta sama

Manyan sojojin Iran aƙall 13 ne suka mutu, ciki har da zaratan soji bakwai na runduna ta musamman ta Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC), a harin da aka ɗora wa Isra'ila alhakin kai shi.

Cikin waɗanda aka kashe har da Janar Mohammad Reza Zahedi, babban kwamanda na Dakarun Quds da ke rundunar IRGC a Syria da Lebanon, da mataimakinsa Janar Hadi Haj Rahemi.

A yayin da Isra'ila ta kwashe fiye da wata shida tana kai hare-hare a Gaza, Katz ya ƙi faɗin takamaimai ranar da dakarun sojinsu za su shiga Rafah da ke kudancin yankin.

"Na san cewa Isra'ila za ta shiga Rafah, amma ba na so na yi ƙarin bayani," in ji shi.

Duk da Allah wadarai da ƙasashen duniya suke yi da Isra'ila kan mawuyacin halin da ta jefa Falasɗinawan da ke Gaza a ciki, tuni firaiministan Isra'ila ya sha alwashin kai hari a Rafah da ke kudancin yankin inda Falasɗinawa kusan miliyan biyu suke samun mafaka.

Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba bayan Hamas ta kai mata harin ba-zata, wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 1,200.

Daga wancan lokaci zuwa yanzu, dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa fiye da 33,300 tare da jikkata sama da mutum 76,000 da kuma lalata galibin gine-ginen da ke Gaza.

AA