A yayin da ake zaman ɗar-ɗar tsakanin Isra'ila da Iran, bayanai sun ce mahukunta a Tehran sun "fito da makamai masu linzami sama da ɗari ɗaya waɗanda ke da gudun gaske domin yiwuwar kai hari" kan Isra'ila, kusan mako biyu bayan Isra'ila ta kai hari a ƙaramin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus inda ta kashe zaratan sojoji bakwai na ƙasar, ciki har da janar-janar guda biyu.
Gidan talbijin na ABC News ya ambato wasu majiyoyi a ma'aikatar tsaron Amurka ranar Juma'a suna cewa gwamnatin da ke Tehran ta shirya makamai masu linzami sama da ɗari don yin ramuwar gayya amma Amurka ta tura ƙarin kayan yaƙi yankin, ciki har da jiragen ruwa da na sama na yaƙi.
A halin da ake ciki Amurka ta aika makaman da ke lalata jiragen ruwan yaƙi zuwa yankin gabas na Bahar Rum da nufin kare Isra'ila, in ji rahoton ABC News.
An sanya wa makaman lalata jiragen ruwan yaƙin na'urori masu inganci, waɗanda za su iya tunkarar duk wata barazana daga makamai masu linzami.
Isra'ila ta shiga shirin ko-ta-kwana bayan Iran ta yi rantsuwa cewa za ta rama harin da ta kai mata ranar 1 ga watan Afrilu a ofishin jakadancin ta da ke Damascus, babban birnin Syria.
A hukumance Isra'ila ba ta fito ta ɗauki alhakin kai harin ba, sai dai ta kwashe watanni tana kai hare-hare kan yankunan da Iran ke iko da su a faɗin Syria.
Iran da ƙungiyar Hezbollah, babbar ƙawarta a Lebanon, sun ce dole Isra'ila ta ɗanɗana kuɗarta sakamakon harin da ta kai wa Iran.
Iran za ta 'kare kanta' daga duk wata barazana ta Amurka
A ɓangare guda, jami'an gwamnatin Amurka biyu da ba sa so a faɗi sunayensu sun shaida wa shafin intanet na Politico cewa Iran tana shirin kai babban hari da ba a saba ganin irinsa ba kan Isra'ila nan da kwanaki kaɗan masu zuwa, "harin da zai haɗa da makamai masu linzami da jiagen yaƙi maras matuƙa."
Dukkan jami'an biyu suna ganin cewa ba zai yiwu Iran ta kai harin ba tare da ta hasala Amurka don mayar da martani ba, domin kuwa duk wani hari da za ta kai zai ƙara zaman ɗar-ɗar a yankin Gabas ta Tsakiya.
"Gwamnatin Biden tana sa rai Iran za ta mayar da martani nan da kwanaki kaɗan masu zuwa — mai yiwuwa a wannan ƙarshen makon," in ji wani jami'i.
Wannan hayaniya tana faruwa ne a yayin da Isra'ila take ci gaba da yin luguden wuta a Gaza tun watan Oktoba da ya wuce inda ta kashe Falasɗinawa fiye da 35,500 — kashi 70 daga cikinsu jarirai da mata da ƙananan yara — sannan ta jikkata fiye da mutum 76,000 baya ga lalata gine-gine da jefa mutanen yankin cikin bala'in yunwa da cututtuka.