"Kowace ƙungiyar Red Crescent, da ke aiki da sauran ƙungiyoyi na ƙasashe, tana samun tagomashi da basira wajen aikin bayar da agaji."  in ji  Yilmaz. / Hoto: AA

Ƙungiyar Bayar da Agaji ta Turkish Red Crescent ta buɗe sabon ofis a Damascus babban birnin Syria, wanda shi ne mataki na biyu da ƙasashen duniya suka ɗauka tun bayan kifewar gwamnatin ƙasar.

An gudanar da bikin buɗe ofishin a hedkwatar Syrian Arab Red Crescent (SARC) wanda shugabar Turkish Red Crescent Fatma Meric Yilmaz da shugaban Syrian Red Crescent Mohammad Hazem, da kuma Janar Darakta kan Bayar da Agaji na Ƙasashen Duniya da Ƙaura na ƙungiyar Turkish Red Crescent Alper Kucuk, da sauran jami'ai suka halarta ranar Asabar.

An yi bikin buɗe ofishin Turkiyya ne a ginin ƙungiyar bayar da agaji ta Syrian Red Crescent.

Kazalika an raba kayan agaji ga mabuƙata bayan buɗe ofishin. Daga bisani Yilmaz da Hazem suka tafi lardin Barzeh da ke Damascus domin kai kayan agaji ga sauran mabuƙata.

Yilmaz ta miƙa wa Hazem wani tambari, inda ta taya shi murnar naɗin da aka yi masa a matsayin shugaban ƙungiyar Syrian Red Crescent.

Ta bayyana gamsuwarta kan yadda ake haɗa kai wajen gudanar da ayyukan agaji, inda ta tuna ayyukan da suka gudanar a baya a yankin Idlib.

Wannan ofis zai taimaka wajen tattara bayanai game da agajin da ake buƙata da kuma yadda za a rarraba shi, a cewar Yilmaz.

"Kowace ƙungiyar Red Crescent, da ke aiki da sauran ƙungiyoyi na ƙasashe, tana samun tagomashi da basira wajen aikin bayar da agaji," in ji ta.

TRT World