Manyan limaman addinin Kiristanci na Syria sun ziyarci Sharaa, shugaban sabuwar gwamnatin ƙasar

Manyan limaman addinin Kiristanci na Syria sun ziyarci Sharaa, shugaban sabuwar gwamnatin ƙasar

Ahmed al Sharaa, shugaban sabuwar gwamnatin Syria ya karɓi baƙuncin manyan limaman addinin Kiristanci.
Shugaban sabuwar gwamnatin Syria, Ahmed al Sharaa ya gana da manyan limaman addinin Kirista a Damascus, Syria ranar 31 ga watan Disamba, 2024. /Hoto: X

Wata tawagar manyan limaman addinin Kiristanci ta gana da Ahmed al-Sharaa, shugaban sabuwar gwamnatin Syria, a gidan gwamnati da ke birnin Damascus.

Wasu hotuna da kamfanin dillancin labaran Syrian News Agency (SANA) ya fitar ranar Talata sun nuna Sharaa yana karɓar baƙuncin wakilan ɗarikun Kiristoci daban-daban na Syria, ciki har da Orthodox, Katolika, Armenian Orthodox, Syriac Orthodox, da furotestan.

An ƙiyasta cewa Kiristoci su ne kashi 10 na al'ummar Syria, wadda yawanta ya kai miliyan 23 kafin ɓarkewar yaƙin basasa a 2011.

A baya sabuwar gwamnatin Syria ta ayyana ranakun 25-26 ga watan Disamba, waɗanda suka yi daidai da lokacin Kirsimeti, a matsayin ranakun hutu.

A ƙasar Syria, mabiya ɗarikar Katolika da Orthodox suna yin bukukuwan Kirsimeti da na Easter tare da na Sabuwar Shekara, a wani mataki na haɗa kan mabiya addinan ƙasar.

Yaƙin basasar Syria ya yi matukar tasiri kan al'ummar Kirista ta ƙasar. A Aleppo, an samu raguwar Kiristoci daga kusan 200,000 a 2011 zuwa 30,000 a yanzu, a cewar shugabanni.

TRT World