Yakin Ukraine ya ta'azzara yawan mutanen da suka rabu da muhallansu a duniya sakamakon bala'o'i inda yawan mutanen ya kai miliyan 71.1 a bara, a cewar wani rahoto na Hukumar Kula da 'Yan gudun Hijira ta Norway, Norwegian Refugee Council.
A karshen shekarar 2022, mutum 5.9 aka tursasa wa barin Ukraine saboda hare-haren sojin Rasha, lamarin da ya sa yawan 'yan gudun hijira sakamakon rikice-rikice ya kai fiye da miliyan 62, abin da ya karu da kashi 17 cikin 100 tun daga 2021.
Syria ce ta fi yawan 'yan gudun hijira da miliyan 6.8 bayan shafe fiye da shekara 10 ana yakin basasa a kasar.
Adadin mutanen da suka rabu da muhallansu a cikin kasarsu a karshen shekarar 2022 saboda bala'o'i irin su ambaliyar ruwa da fari ya kai miliyan 8.7, inda ya karu da kashi 45 cikin 100 daga shekarar 2021.
Jimillar mutum miliyan 71.1 da yakin ya daidaita a fadin duniya ya kai kashi 20 cikin 100 tun shekarar 2021.
Ba a samu saukin kwararar 'yan gudun hijira ba sakamakon yakin Ukraine da Syria da Habasha da ma wasu wuraren a 2023.
A makon nan Hukumar Kula da Kaurar Jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tuni karin mutum 700,000 suka zama 'yan gudun hijira cikin makonni kadan da fara rikici a Sudan tsakanin rundunar sojin kasar da dakarun da ba na gwamnati ba RSF.
Wata cibiya mai sa ido kan gudun hijirar jama'a ta bayyana sauyin yanayi da ake fama da shi a matsayin daya daga cikin bala'o'in da ke tursasa wa mutane rabuwa da muhallansu.
Lamarin ya janyo ambaliyar ruwa a kasashe irin su Pakistan da Nijeriya da Brazil da kuma mummunan farin da ake fama da shi a Somaliya da Kenya da Habasha.