Sojojin gwamnatin Siriya hudu ne suka mutu, yayin da wasu hudu suka jikkata a wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai a kusa da babban birnin kasar Damascus da sanyin safiyar ranar Litinin, a cewar rahoton da kamfanin dillancin labaran kasar SANA ya fitar.
Da misalin karfe 2:20 na safe (23:20 agogon GMT a ranar Lahadi) dakarun makiyarmu Isra'ila sun kai hari ta sama daga wajen yankin Golan na Siriya da aka mamaye, inda suka nufi yankunan da ke kusa da birnin Damascus, in ji ratohon na SANA.
Harin ya kashe "sojoji hudu tare da raunata wasu hudu", in ji rahoton da bai fayyace girma barnar da harin ya haifar ba, ya kuma kara da cewa sojojin saman Siriya sun kama wasu makamai masu linzami.
Wakilin AFP a babban birnin kasar ya ruwaito jin karar fashewar wasu abubuwa.
A yakin basasar da aka shafe sama da shekaru goma ana yi a Siriya, Isra'ila ta kaddamar da daruruwan hare-hare ta sama a kan kasar, inda take mai da hankali kan dakarun da Iran ke mara wa baya da mayakan Hezbollah da kuma sansanonin sojojin gwamnatin Siriya.
Ba kasafai Isra'ila ke tsokaci kan hare-haren da take kai wa Siriya ba, amma ta sha nanata cewa ba za ta bari babbar abokiyar adawarta Iran ta fadada ikonta zuwa can ba.
A ranar 19 ga watan Yuli ne harin da Isra’ila ta kai ta sama kusa da birinin Damascus ya kashe mayakan gwamnati uku tare da raunata wasu hudu, a cewar wata majiya da ke sa ido kan yaki a lokacin.
Suka da Allah wadai
Kamfanin dillacin labaran kasar SANA ya ruwaito majiyar sojan kasar na cewa sojojin gwamnatin Siriya hudu ne suka mutu, yayin da wasu hudu kuma suka jikkata a wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai a kusa da babban birnin kasar Damascus da sanyin safiyar ranar Litinin.
Ma'aikatar harkokin waje ta gwamnatin Assad ta yi Allah wadai da "kakkausar murya" kan harin.
A wata sanarwa da SANA ta fitar, ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Sulhu da su dauki matakin gaggawa don tilasta wa Isra'ila "dakatar da wadannan ayyuka ko tsari na ta'addanci".
A farkon watan jiya ne kafafen yada labaran gwamnatin kasar suka ce Isra’ila ta kai hare-hare ta sama kusa da birnin Homs da ke karkashin ikon gwamnati.
Daga baya sojojin Isra'ila suka ce sun kai hari ne kan na'urar kakkabo jiragen sama bayan harba makamin roka.
A ranar 14 ga watan Yuni, Isra'ila ta kai wasu hare-hare ta sama a kusa da Damascus inda ta raunata wani sojan gwamnati, a cewar SANA.
Hare-haren baya-baya da Isra'ila ta kai sun yi sanadin hana filayen jiragen saman Damascus da Aleppo daina aiki.