Türkiye
Turkiyya na son zaman lafiya a Siriya kuma tana goyon bayan yankinta - Altun
Fahrettin Altun ya sake jaddada shirin Shugaba Erdogan na tattaunawa da shugaban gwamnatin Siriya Assad, yana mai cewa tattaunawar tana da muhimmanci a yanayin da ake ciki na rikice-rikice da tashin hankali da kuma gudun hijira.Türkiye
Jami'an leken asirin Turkiyya na ci gaba da fatattakar manyan 'yan ta'addar PKK
Bayan harin ta'addancin da 'yan PKK suka kai a baya-bayan nan da ya yi sanadin mutuwar sojoji 12 a yankin da ake gudanar da ayyukan "Operation Claw-Lock", dakarun Turkiyya sun kai hari wurare da dama na 'yan ta'adda a arewacin Iraki da Siriya.Duniya
Jirgi mara matuki ya kashe mutum 80, ya raunata 240 a taron bikin sojojin Syria
Mintuna kadan bayan barin Ministan tsaron gwamnatin Siriya wurin taron bikin yaye dalibai a birnin Homs, jirage marasa matuki dauke da makamai suka fara harba ruwan bama-bama a kan cincirindon taron, a cewar jami'an tsaro.Türkiye
Turkiyya ta gargadi kasashe kawayenta da su guji kusanci da kungiyar ta'addanci ta PKK/YPG
Sanarwar ma'aikatar ta biyo bayan ayyana wasu cibiyoyin kungiyar ta'addanci na PKK/YPG a kasar Iraƙi da Siriya a matsayin wuraren kai hare-hare kan dakarun Turkiyya, tana mai gargadin ƙasashe ƙawayenta da su ƙaurace yin duk wata alaƙa da ƙungiyar.
Shahararru
Mashahuran makaloli