| Hausa
TURKIYYA
2 MINTI KARATU
Turkiyya ta mayar da bakin haure sama da 30,000 kasashensu a 2023
Sama da ‘yan kasar Afganistan 955 aka mayar gida a tsakanin takwas zuwa 12 ga Afrilu, in ji Hukumar Kula da Shige da Fice ta Turkiyya.
Turkiyya ta mayar da bakin haure sama da 30,000 kasashensu a 2023
Turkiyya na yunkurin hana bakin haure shiga teku don tafiya zuwa kasashen Turai / Hoto: AA / AA
12 Afrilu 2023

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Turkiyya ta ce da mayar da bakin haure 30,527 zuwa kasashensu.

Sanarwar da Hukumar ta fitar ta ce “Muna ci gaba da yaki da gudun hijira ba bisa ka’ida ba, kuma muna ci gaba da mayar da bakin haure zuwa kasashensu.”

A shekarar da ta gabata an mayar da bakin haure 124,441 zuwa kasashensu a jiragen sama 237 da aka yi shata.

Bakin hauren sun hada da ‘yan kasar Afganistan 235, da wasu kuma da aka mayar zuwa Pakistan.

Turkiyya ta zama hanya mai muhimmanci da ‘yan gudun hijira ke yada zango a yunkurin da suke na isa Turai don smaun ingantacciyar rayuwa da kuma gujewa rikice-rikicen da ake yi a kasashensu.

MAJIYA:AA