Assad da iyalansa sun gudu daga Siriya zuwa Moscow, bayan 'yan adawa sun kwace iko da babban birnin Sham / Photo: AFP

Kasashen Larabawa da dama sun ti maraba da kawo karshen mulkin Bashar Al Assad, inda suka yi kira da a tabbatar da zaman lafiya da ci gaba, tare da kare yanayin da aka shiga ya koma rikici babba.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta fitar kasar ta ce suna “sanya idanu kan abubuwan da ke wakana cikin gaggawa a kasar ‘yar'uwa gare su.

"Kuma sun gamsu da irin matakan da aka dauka na tabbatar da zaman lafiyar Siriyawa, kare afkuwar zubar da jini da tsare dukiyoyi da hukumomin Siriya.”

Saudiyya ta yi kira ga kasashen duniya da su “tashi su goyi bayan jama’ar Siriya amma su guji tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar.”

A Qatar, Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar da sanarwa inda ta ce Doha “na bin diddigin al’amiran da ke wakana a Siriya” kuma ta zayyana cewa “dole ne a kare hukumomin kasa da hadin kan kasar domin hana kasar fada wa rikici.”

Qatar ta bayyana bukatar a kawo karshen rikicin Siriya ta hanyar aiki da Hukuncin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2254, ta hanyar da “za ta biya bukatar jama’ar Siriya tare da kuma kare hadin kai, ‘yancin mulki da gudanarwar kasar.”

Ma’aikatar Harkokin Waje ta Bahrain ma ta fitar da sanarwa, inda ta yi tsokaci da cewar Manama na bin diddigin me ke wakana a Siriya, “tana jaddada goyon bayan tabbatar da tsaro, kwanciyar hankali, da tsare martabar iyakokin Siriya.”

Ta yi kira ga dukkan bangarori na jama’ar Siriya da su bayar sa fifiko ga bukatun kasar da kuma walwala da jin dadin jama’a, tare da tabbatar da kare cibiyoyin gwamnati da tsare muhimman kayayyakin da ke habaka tattalin arziki.

‘Fifita bukatun kasa'

Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta ce Alkahira “na bibiya tare da sanya idanu matuka kan sauyin da aka samu a Siriya” ta kuma jaddada goyon bayanta ga ‘yancin mulki na Siriya, martabar iyakokinta da hadin kan al’ummar kasar.

Ta yi kira ga “dukkan bangarorin da ke Siriya, ba tare da duba ga akidarsu ba, su kare kadarori da kayan gwamnati, sannan su bayar da fifiko tare da samar da tsarin siyasa da zai tafi da kowa domin assasa sabon shafin da zai kawo zaman lafiya a cikin gida, da dawo da matsayin Siriya a yankin da duniya baki daya.”

A Jordan, Sarki Abdullah II ya ce kasarsa “na tare da jama’ar Siriya kuma tana girmama ra’ayi da zabin su,” kamar yadda sanarwar da aka fitar gaga Masarautar ta bayyana.

Sarki Abdullah a wajen wani Taron Tsaro na Kasa ya jadda cewa “muna bukatar tabbatar da tsaro a Siriya da kare ‘yan kasa da kuma aiki cikin gaggawa don tabbatar da kwanciyar hankali da kare barkewar rikici.”

Kazalika, Majalisar Shugaban Kasar Yemen tabtaya al’ummar Siriya murna saboda rushewaf gwamnatin Assad.

Yemen ta sake tabbatar da matsayinta, goyon bayan ‘yancin iyakokin Siriya, girmama ‘yancin cin gashin kanta da bukatar ‘yanci, sauyi, zaman lafiya da kwanciyar hankalin jama’ar Siriya.

'Tattaunawa tsakanin dukkan bangarori’

A Iraki, kakakin gwamnati Basim Al Awadi a wata sanarwa ya ce Iraki “na bibiyar al’amuran da ke afku wa a Siriya kuma tana ci gaba da tuntubar kasashe ‘yan'uwa da abokai don yin kokarin tabbatar da kwanciyar hankali, tsaro, bin doka da oda da kare rayuka da dukiyoyin jama’ar Siriya.”

Irak ta jaddada muhimmancin kar a tsoma baki a harkokin cikin gidan Siriya ko a goyi bayan wani bangare sama da wani, saboda wannan zai janyo karin rikici da rabuwar kai a kasar.”

A wata sanarwa, Aljeriya ta bayyana goyon bayanta ga jama’ar Siriya, tana mai jaddada babbar alakar da ke tsakanin al’ummun kasashen da kuma tarihin da suke da shi iri guda.

Ta yi kira ga “a yi tattaunawa tsakanin dukkan bangarorin jama’ar Siriya, fifita manyan bukatun kasar, kare albarkatun kasa, da gina makomar da za ta rungumi kowa a hukumomin da za su bayyana me al’ummar Siriya ba tare da tsoma bakin kasashen waje ba.”

Fadar shugaban kasar Falasdin ta ce “Falasdin da jama’arta na tare da al’ummar Siriya, suna girmama zabinsu na siyasa da me suke bukata, tabbatar da tsari, kwanciyar hankali, da kuma kare nasarorin da suka samu," in ji sanarwar da kamfanin dillancin labarai na Falasdin WAFA ya fitar.

Sanarwar ta jaddada muhimmancin "dukkan bangarorin siyasa na su bayar da fifiko ga bukatar jama'ar Siriya, a tabbatar da dawo da muhimmiyar rawar da Siriya ke taka wa a yankin da ma duniya baki daya, wanda ke da amfani ga manufofin Falasdinawa da gwagwarmayar neman 'yanci da suke yi."

TRT Afrika