Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira da a kara karfafa da samar da tabbatacciyar alakar Turkiyya da Tarayyar Turai, yana mai jaddada Turkiyya na ci gaba da kokarin ganin an cimma wannan manufa a matsayinta na 'yar takara da ke son shiga Tarayyar.
Kalaman na shugaban na zuwa ne a wajen taron manema labarai na hadin gwiwa da Shugabar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen a fadar shugaban kasa da ke Ankara a ranar Talata.
Erdogan ya bayyana fatan Tarayyar Turai za ta dauki manyan matakai wajen sabunta yarjejeniyar Kungiyar Fito tare da hanzarta tsarin janye Visa gaba daya ga 'yan turkiyya don shiga kasashen Tarayyar
"Kada a kankantar da alakar Turkiyya da Turai ga kananan batutuwan wasu mambobin Tarayyar', in ji Erdogan, yana mai karin haske kan bukatar da ke akwai ta samun tsarin daidaito tsakanin Turkiyya da Tarayyar Turai.
Bukatar neman shiga Tarayyar Turai da Turkiyya ta bayyana a 2005 ta samu tsaiko a 2007 saboda rikicin Tsibirin Cyprus da yadda mambobin Tarayyar da dama suke adawa da shigar Turkiyya kawancen.
Tabbatar da 'yancin mulki na SIriya
Game da batun yankuna, Erdogan ya bayyana muhimmancin ci gaba da kare martabar 'yancin mulki da iyakokin Siriya da kafa gwamnatin da za ta tafi da kowanne bangare a kasar da yaki ya tagayyara.
"Mun ga yadda muke da ra'ayi iri guda game da kare martabar 'yancin mulki da iyakokin Siriya da kafa gwamnatin da za ta kunshi kowa." in ji Erdogan yana nufin von der Leyen.
Erdogan ya kuma bayyana rawar da Turkiyya ke taka wa wajen yaki da ta'addanci, yana mai cewar Turkiyya ce kasa mambar NATO da ta yi nasara kan 'yan ta'addar PKK da Daesh a fagen daga.
Shugabar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce suna sane da damuwar Turkiyya kan tsaro.
Ta kuma yi nuni da cewa Tarayyar Turai ce ta fi baiwa Siriya gudunmowa inda ta yi kira da a mayar da hankali wajen sake gina kasar.
"Dole ne tallafin Tarayyar Turai ya mayar da hankali ga sabon salo, kuma muna bukatar mayar da hankali kan sake gina kasar," in ji von der Leyen.