Ministan wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu (Dama), Ministan wajen Rasha Sergey Lavrov (na biyu daga hagu), Ministan wajen Siriya Faisal Mikdad (na biyu daga dama) da Ministan wajen Iran Hossein Amir Abdollahian (Hagu) sun halarci taron da aka yi a Moscow. / Hoto: AA 

Ministocin harkokin wajen Turkiyya, Rasha, Iran da Siriya sun yanke shawarar samar da wani shiri da zai inganta alakar Turkiyya da Siriya, a cewar wata sanarwar hadin-gwiwa da aka fitar.

A ranar Larabar nan ne a birnin Moscow, ministocin harkokin wajen Turkiyya, Rasha, Iran da Siriya suka gudanar da taro.

Ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta bayyana cewa a yayin taron, mahalarta sun yi musayar ra’ayi kan kokarin daidaita alakar Turkiyya da Siriya, sun kuma tattauna batutuwan yaki da ta’addanci, matakan siyasa da ayyukan jinkai da dawowar 'yan Siriya gida bisa radin kansu cikin girmamawa.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta kuma ce “Mahalarta taron sun kuma sake tabbatar da girmama ‘yancin mulkin Siriya, darajar iyakokinta da kuma yaki da ta’addanci yadda ya kamata, yin la'akari da Matakin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2254 da kuma sanarwar da aka fitar a hukumance bayan taron Astana."

An kaddamar da tsarin Astana a 2017 don dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Siriya da rikici ya tagayyara tun bayan zanga-zangar masu rajin dabbaka dimokuradiyya a 2011.

Samar da hanyar inganta alaka

Sanarwar ta kara da cewa, bangarorin hudu sun amince da umartar mataimakan ministocin harkokin wajensu da su samar da wani shiri da zai gyara alakar Turkiyya da Siriya, inda za su hada kai da ma’aikatun tsaro da hukumomin leken asiri na kasashen don samar da shirin.

Sanarwar ta ce ministocin harkokin wajen su hudu sun amince da su ci gaba da tuntubar juna, inda suka kara da cewa tattaunawar Moscow ta wanzu a yanayi mai kyau da bayar da ma'ana.

A wani sako da ya fitar ta shafin Twitter bayan taron, ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya ce taron nasu ya jaddada muhimmancin hadin kai wajen yaki da ta’addanci, aiki tare da samar da yanayin da Siriyawa za su koma kasarsu, bayar da muhimmanci ga harkokin siyasar Siriya da kuma martaba iyakokinta.

A watan Disamban da ya gabata, ministocin tsaro da shugabannin hukumomin leken asiri na Turkiyya, Rasha da Siriya sun gana a Moscow tare da amince wa kan ci gaba da tattauna war bangarorinsu uku don tabbatar da zaman lafiya a Siriya da yankin baki daya.

An saka Iran a tattaunawar saboda a baya gwamnatin Ankara ta bayyana "Za ta ji dadi idan aka saka Iran a wannan yunkuri".

Tun 2011 yakin basasa mummuna ya faro a Siriya a lokacin da gwamnatin Assad ta dinga amfani da karfin da ya wuce kima wajen murkushe masu rajin dabbaka dimukradiyya da ke zanga-zanga.

TRT World