Sojojin Amurka na bayar da horon soji ga 'yan kungiyar ta'addar PKK/YPG, matakin da Turkiyya ta ce ya kara fadada ayyukan PKK a Siriya.

Turkiyya ta buƙaci ƙasashe musamman ƙawayenta da su guji yin duk wata alaƙa ta kusanci da ƙungiyar ta'addanci ta PKK/YPG, a cewar wata sanarwa da majiyar Ma'aikatar Tsaron ƙasar ta fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta biyo bayan ayyana wasu cibiyoyin ƙungiyar PKK/YPG a kasar Iraƙi da Siriya a matsayin wuraren kai hare-hare na ƴan ƙungiyar kan dakarun Turkiyya da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi.

Fidan ya gargaɗi wasu ɓangarori uku - ba tare da ya bayyana sunayensu ba - da su nisanci wuraren ayyukan PKK/YPG.

Da aka tambayi majiyar kan ko wannan sabon gargaɗi ne Fidan ya fitar, sai ta ce " tunatarwa ce, da kuma kira ga taka tsantsan ga wadanɗa lamarin ya shafa."

Turkiyya ta ƙara zafafa kai hare-hare kan ayyukan ƙungiyar PKK/YPG a yankunanta da kuma maƙwabtanta Siriya da Iraƙi, bayan da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tarwatsa kansa a gaban harabar babban ofishin tsaro da ke Ankara, babban birnin ƙasar Turkiyya a ranar Lahadi.

Jami’an tsaro dai sun yi nasarar kashe ɗaya daga cikin ƴan ta’addan da suka kai harin a harabar shiga ofishin.

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Turkiyya ta tabbatar da alaƙar maharan da ƙungiyar ta'addanci ta PKK/YPG.

"Muna jaddada cewa ƙungiyar PKK/YPG daya take da ƙungiyar ƴan ta'adda, kuma duk inda suke aiki, nan za mu dinga kai hare-harenmu," a cewar majiyar Ma'aikatar Tsaron.

"A ko yaushe muna ƙara jaddada cewa ka da sauran ƙasashe, musamman ƙawayenmu da wadanda muke da alaƙa, da ka da su kusanci waɗannan 'yan ta'addan."

Amurka na taimakon PKK/YPG a arewacin Siriya

YPG shi ne reshen ƙungiyar ta'addanci ta PKK da ke Siriya, ta kwashe sama da shekara 35 tana kai hare-haren ta'addanci kan Turkiyya.

Kasashen ƙungiyar Tarayyar Turai da Turkiyya da kuma Amurka sun sanya PKK a jerin sunayen ƴan ta'adda da suka ɗorawa alhakin mutuwar mutum sama da 40,000 da suka haɗa da mata da yara da kuma jarirai.

Ankara ta daɗe tana kira ga Washington da ta daina ba da horon soji da kuma bai wa ƙungiyar ta'addanci makamai, ciki har da manyan makamai da za a iya amfani da su kan jami'an tsaron Turkiyya da fararen hula.

A ɓangare guda Amurka ta ce tana ƙawance da ƙungiyar ne domin yaƙar ƙungiyar ta'addanci ta Daesh, batun da Turkiyya ta ce babu ma'ana a yi amfani da wata ƙungiyar ta'addanci wajen yaƙar wata kungiyar irinta.

Tun a shekarar 2015 ne Amurka da dakarun ƙawancen da take jagoranta suka bai wa ƴan ta'addar YPG/PKK horo da makamai.

Kazalika Sojojin Amurka sun yi ta gudanar da atisayen haɗin gwiwa da ƴan ta'addar YPG/PKK a cikin yankunan hamada.

TRT World