Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bukaci majalisar mai kasashe mambobi 193 da ta kafa sabuwar cibiyar kasa da kasa da za ta mayar da hankali wajen fayyace makomar 'yan Siriya 100,000 da suka bata.
A ranar Talata ne Guterres ya bayyana cewa, 'yan Siriya na da hakkin sanin gaskiyar inda 'yan uwansu suke.
"Adalci ya bukaci hakan, domin samun zaman lafiya da sulhu duk sun dogara kan hakan," in ji Guterres a jawabinsa ga mambobin majalisar.
Kimanin mutum 100,000 ne suka bata tun a lokacin da aka fara yakin basasar kasar a shekarar 2011, inda aka murkushe masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a zamanin juyin juya halin kasashen Larabawa.
Wannan lamari ya shafi mutane da dama a kowane yanki da kabila da ke fadin kasar, wadanda ke da 'yan uwa da suka bata, ciki har da wadanda aka tilasta musu tserewa ta hanyar azabtarwa ko garkuwa da su ko aka ci zarafinsu.
‘’Dole mu kara azama tare da gaggauta aikin magance wannan mummunan yanayi. Siriyawa sun cancanci a kawo musu dauki," in ji Guterres,
Babban jami'in kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk ya ce rikicin wanda ya cika shekara 13 da faruwa, wani salo ne na take hakkin bil’adama.
‘’Yana da wuya a iya tabbatar da adadin yawan mutanen da suka bata a Siriya. An dai bayar da adadin mutum 100,000 ne kawai don kwatantawa, amma ainihin yawan mutanen zai iya zarta hakan.
Dole ne cibiyar da za a kafa din ta kasance a wurin da 'yan uwa da iyalan wadanda lamarin ya shafa za su samu kwanciyar hankali da tabbacin samun bayanan kariya,’’ in ji Turk.
Turk ya kuma kara da cewa ‘’Yara suna dada girma a wuraren da ya kamata mahaifansu maza suke, suna kuma ganin yadda iyayensu mata da 'yan uwansu mata ke kokarin tallafawa rayuwarsu.’’
Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres
Ya ce, ba za a taba samun dauwamammen zaman lafiya a Siriya ba idan ba a samu wani ci gaba kan batun mutanen da suka bata ba.
Ya bukaci MDD da ya yi la'akari da kafa sabuwar hukumar da za ta samar da duk wasu bayanai kan abin da ya faru ga dukkan mutanen da suka bata.
"Al'ummar Siriya na bin mu bashi," in ji shi.