Mahukuntan Turkiyya na amfani da kalmar ''kawarwa'' ga 'yan ta'addan da  suka mika wuya ko kuma aka kashe su ko kuma aka kama su. / Hoto: AA  

Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya MIT ta yi nasara wajen kawar da babban ɗan ta'adda mai suna Erdinc Bolcal, da aka fi sani da Ali Xebat, wanda ke jagorantar makarantar Slilan Guyi Academy da ke ba da horo kan ayyukan ƙungiyar ta'addanci ta PKK.

An kawar da Erdinc Bolcal ne a wani aikin samame da aka kai yankin Sulaymaniyah, inda ya ke yaɗa aƙida tare da ba da horo kan ayyukan soji ga 'yan ta'addan da za su shiga ayyukan ƙungiyar PKK na shirin kai wa Turkiyya da dakarunta da ke aiki a Iraƙi hare-hare, a cewar sanarwar kafofin tsaro a ranar Litinin.

Bolcal na ba da horo kan aƙida da dabarun kutse cikin manyan biranen Istanbul da Izmir a madadin ƙungiyar PKK, sannan ya kasance yana yaɗa farfaganda tare da matsa wa matasa lamba a yankunan karkara don su shiga cikin ƙungiyar ta'addancin.

Bolcal na hannun hagu, shi ne dan ta'addan ke ba da horon kan dabaru kai hare-hare a manyan biranen Istanbul da Izmir a madadin kungiyar ta'adda ta PKK.

Bayan shafe wasu tsawon lokuta yana aiki a madadin ƙungiyar, Bolcal ya kutsa kai zuwa arewacin Iraƙi, inda ya aiwatar da ayyukan da suka shafi ta'ammali da makamai tare da ɗaukar nauyi.

Ya ci gaba da aiwatar da ayyukan a matsayin wanda ake kira da kwamandan rundunar sannan jagora da ke riƙe da wurin ba da horo na yankin Sulaymaniyah da Kirkuk.

Ƙarƙashin wani aikin haƊin gwiwa na hukumar leƘen asiri ta Turkiyya MIT, an gano cewa 'yan ta'addan suna shirin kai hari kan matsugunin Turkiyya a Kirkuk, a cewar majiyar tsaron.

Turkiyya za ta biya ko nawa ne "duk tsada" don daƘile ayyukan ta'addanci

Tun bayan harin ta'addancin da 'yan ta'addar PKK suka kai a ranar Juma'a, wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin Turkiyya 12, hare-haren da jiragen saman Turkiyya suka kai sun lalata wuraren ayyukan ta'addanci da dama a yankin arewacin Iraki da Siriya.

Cikin sabon matakin yaki da ta'addanci da Turkiyya ta dauka, kasar ta yi sanarar kawar da jimillar 'yan ta'adda 56.

A ranar Asabar, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sha alwashin cewa, Turkiyya za ta biya ko nawa ne "duk tsada" don dakile ayyukan ta'addanci a yankin arewacin Iraki da Siriya.

Kazalika Ma'aikatar tsaron kasar ta sanar a ranar Litinin cewa, jami'an tsaron Turkiyya sun kawar da wasu 'yan ta'addar PKK 26 a arewacin Siriya da Iraƙi.

A mafi yawan lokuta 'yan ta'addar PKK kan fake a arewacin Iraƙi domin shirya kai hare-haren wuce gona da iri kan Turkiyya. An fi sanin reshen kungiyar PKK da ke Siriya da YPG.

Turkiyya ta ƙaddamar aikin Operation Claw-Lock a watan Afrilun 2022 don kai hari kan maboyar 'yan ta'addar PKK a yankunan Metina da Zap da Avasin-Basyan da ke yankin arewacin Iraƙi da ke kusa da iyaka da Turkiyya.

A sama da shekaru 35 da ta shafe tana gudanar da ayyukan ta'addanci kan Turkiyya, ƙungiyar EU da Amurka da ita kanta Turkiyya sun ayyana PKK a matsayin ƙungiyar ta'addanci - sannan an ɗora mata alhakin mutuwar mutum fiye da 40,000 wadanda suka hada da mata da yara da kuma jarirai.

TRT World