Ahmed, wadda aka ce tana da alhakin sayo da kuma amfani da makamai masu linzami ga kungiyar ta'addanci, kazalika ita ta ba da umarnin kai harin makami mai linzami kan jami'an tsaron Turkiyya a Operation Reshen Zaitun daga Tel Rifaat. / Hoto: AA      

Hukumar Leƙen Asiri ta Turkiyya (MIT) ta ''kawar'' da wata jagorar ƙungiyar ta'addanci ta YPG-YPJ a arewacin Siriya, kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana.

An kama Emine Seyid Ahmed a wani aikin samame da aka kai birnin Qamishli a ranar Talata.

Ƴar ta'addar ta kasance tare da ƙungiyar ta'addanci tun daga shekarar 2011, kana an gano ta a matsayin wacce ta kitsa ayyukan da ake kai wa jami'an tsaron Turkiyya.

Hukumomin Turkiyya suna amfani da kalmar “kawarwa” kan ƴan ta'aadan da suka mika kansu ko aka kashe su ko kuma aka kama su.

Emine Seyid, wacce ake zarginta da alhakin sayo da kuma amfani da makamai masu linzami ga ƙungiyar ta'addancin, ita ta ba da umarnin kai harin makami mai linzami kan jami'an tsaron Turkiyya da ke aikin ''Operation Olive'' a yankin Tel Rifaat.

Kazalika an tabbatar da cewa, ƴar ta'addar ce ta ba da umarnin kai wani harin makami mai linzami kan fararen hula a lardin Kilis da ke kudancin Turkiyya.

A sama da shekaru 35 da ta kwashe tana gudanar da ayyukan ta'addancin kan Turkiyya, ƙungiyar PKK - wanda Turkiyya da Amurka da Birtaniya da kuma ƙungiyar Tarayyar Turai EU suka sanya ta a matsayin kungiyar ta'addanci.

Kungiyar ta dauki alhakin mutuwar mutane fiye da 40,000, ciki har da mata da yara da kuma jarirai.

Kungiyar YPG-YPJ rashen PKK ne a Siriya.

TRT World