Shugaban Sashen Watsa Labarai na Turkiyya Fahrettin Altun ya jaddada gagarumar rawar da Ankara ke takawa wajen warware rikicin Siriya da kuma magance tashe-tashen hankula a yankin yayin da a bangare guda ya yi kakkausar suka kan munafunci da kuma nuna son kai da kafafen yada labarai na Kasashen Yamma suke nunawa kan yakin da ake ci gaba da yi a yankin Gaza na Falasdinu.
Altun ya bayyana ƙokarin Turkiyya na inganta zaman lafiya a Siriya tare da Allah-wadai da yadda duniya ke nuna halin ko-in-kula game da wahalhalun da Falasdinawa suke ciki a hirar da jaridar Turkiyya ta yi da shi.
Ya jadadda matsayin Turkiyya na zama muhimmiyar ƙasa mai fada a ji a yankin, wadda ke ƙokarin samar da hanyoyin tsagaita wuta a rikicin Siriya.
A ƙarin haske da yi game da shirin Shugaba Recep Tayyip Erdogan na tattaunawa da shugaban gwamnatin Siriya Bashar Al Assad, Altun ya ce tattaunawar tana da muhimmanci a yanayin rikice-rikice da tashin hankali da kuma gudun hijira da ake ciki.
''Mun kuɗuri aniyar inganta wani tsari bisa ga ka'aidojin yaki da ta'addanci domin tabbatar da 'yancin yankin Siriya, tare da ci gaba da aiwatar da tsarin kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 2254 da aka kafa karkashin ikon Siriya, da kuma samar da yanayi mai aminci," in ji shi.
Kazalika Altun ya jaddada cewa waɗannan ka'idoji za su mayar da hankali wajen magance tushen matsalolin Siriya. Yana mai cewa, dole a samar da tattaunawa ta gaskiya tsakanin bangorin Siriya, kamar yadda kudurorin kwamitin sulhu na MDD suka zayyana.
Turkiyya na ci gaba da jajircewa wajen yaki da ayyukan ta'addanci, tare da tabbatar da tsaron mutanen da suka rasa matsugunansu, da kuma samar da zaman lafiya a yankin.
"Turkiyya tana da riba mai yawa da za ta samu kan ƙudurin zaman lafiyar Siriya, kuma mun himmatu wajen cim ma wannan tsarin," a cewar Altun.
Zalunci a Gaza
Yayin da yake magana kan yakin Gaza, Altun ya yi Allah-wadai da bala'in jinƙai tare da zargin gwamnatocin Ƙasashen Yamma da nuna son kai da kuma kafafen yada labaransu.
"Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, ya bayyana a fili cewa dabi'un Ƙasashen Yamma kamar 'yancin ɗan'adam da 'yancin aikin jarida sun shafi tsirarun ƙasashe ne waɗanda ke da ra'ayi irin nasu," in ji Altun.
Altun ya kuma zargi Isra'ila da yin amfani da bayanan karya don tabbatar da kuma wanke ayyukanta a idon duniya.
Kazalika ya yi waiwaye kan ƙaryar da shugaban Isra'ila Isaac Herzog ya sharara a taron tsaro na Munich, inda Herzog ya yi zargin cewa wani littafi da aka samu a Gaza ya ingiza aikata kisan kiyashi kan Yahudawa.
Cibiyar yaki da labaran ƙarya ta Turkiyya ta fallasa wannan zargi a matsayin ƙage, inda ta bayyana cewa littafin wanda aka wallafa daga ƙasar Masar a shekarun 1990, ba shi da alaƙa da Falasdinu ko Hamas.
"Wannan karyar da aka sharara, kafafen yada labarai na kasashen yamma ne suka yada ta, da nufin karkatar da gaskiya da kuma bayyana Falasdinawa a matsayin masu aikata kisan kiyashi," in ji Altun.
Kira don sake fasalin ƙasa da ƙasa
Altun ya sake jadadda ƙiran da shugaba Erdogan ya yi kan a yi wa harkokin shugabancin duniya garambawul, inda ya bayar da shawarar samar da tsarin da ya dace don magance matsaloli kamar mamayar da Isra'ila ke yi wa yankunan Falasdinawa cikin gaggawa.
Altun ya jaddada rawar da Turkiyya ke takawa a manyan taruka kamar G20, wanda ya bayyana shi a matsayin muhimmin wajen magance kalubalen da duniya ke fuskanta kamar tsaron abinci da gudun hijira da sauyin yanayi.
''Kamar yadda ta saba, Turkiyya za ta sauke nauyin da ke kanta, tare da yin aiki da kungiyoyi masu tasiri kamar G20 don daidaita tsarin kasa da kasa da ke kara samun rauni," in ji shi.