Wani hari da jirgi mara matuki ya kai a kan taron bikin yaye daliban sojojin kasar Siriya a birnin Homs ya kashe mutane 80 tare da raunata 240.
Harin na daya daga cikin mafi muni a baya-bayan nan da aka kai kan sojojin gwamnatin kasar, wadanda suka shafe fiye da shekaru goma suna yakin basasa.
A wata sanarwa da rundunar sojin Siriya ta fitar a baya ta ce jiragen yaki marasa matuki dauke da bama-bamai sun kai hari kan taron bikin da ya hada jami'anta matasa da iyalansu a daidai lokacin da ake kokarin kammala bikin.
Ba tare da bayyana sunan wata kungiya ba, rundunar sojin ta zargi ''yan' tayar da kayar baya'' wadanda suka samu goyon bayan dakarun kasashen waje da kai harin, ta kuma ce za ta mayar da martani da ''dukkan karfi da azama'' kan kungiyoyin ta’addanci a duk inda suke.
Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai harin a daidai lokacin da kasar Siriya ke fama da yakin shekaru 13.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres "ya nuna matukar damuwa" game da harin jiragen yaki mara matuki da aka kai birnin Homs da kuma rahotannin harin ramuwar gayya a arewa maso yammacin Siriya, in ji kakakinsa Stephane Dujarric.
Damascus ta sanar da zaman makoki na kwanaki uku wanda za a fara ranar Juma'a.
Hare-hare a Idlib
Birnin Homs ya kasance yankin da ke karkashin ikon gwamnati kana yana da nisa daga fagen dagar da dakarun gwamnati da na 'yan adawa suka saba fafatawa.
Bayan harin da jirgin, sojojin Siriya sun yi ta luguden wuta a kauyukan lardin Idlib da ke arewa maso yammacin kasar da ke hannun 'yan adawa.
A garuruwan Al Nayrab da Sarmin da ke gabashin birnin Idlib, akalla fararen-hula 10 ne suka ji rauni, kamar yadda kungiyar kare-fararen hula ta Siriya da ke hannun ‘yan adawa a arewa maso yammacin kasar da aka fi sani da White Helmets ta bayyana.
Karanta labari mai alaka: Turkiyya ta kai hare-hare da dama kan 'yan ta'adda a Syria
Dakarun gwamnatin kasar sun ci gaba da luguden wuta kan wasu yankunan da ke karkashin ikon 'yan adawa.
Kazalika dakarun sun yi luguden wuta a wani kauye da ke yankin a safiyar ranar Alhamis kafin harin jirgi mara matuki da a kai birnin Homs, a kalla fararen hula biyar ne su mutu, a cewar wasu masu fafutuka da ma’aikatan agajin gaggawa.
Harin ya afka kan wani gidan iyali da ke wajen kauyen Kafr Nouran a yammacin lardin Aleppo, a cewar White Helmets.
Yaki na tsawon shekaru da raba al'umma daga matsuguninsu
Mafi yawan mutane kusan miliyan 4.1 da ke zaune a arewa maso yammacin Syria na rayuwa cikin talauci yayin da suke dogaro kan taimakon jin kai don samun tsira.
Yakin basasar dai ya soma ne daga zanga-zangar lumana ta adawa da gwamnatin Bashar al Assad na Siriya a watan Maris din shekarar 2011, amma sannu a hankli ya rikide zuwa yakin basasa bayan da Assad ya murkushe masu zanga-zangar.
Yakin ya koma goyon bayan Assad a kan kungiyoyin 'yan adawa a shekarar 2015, sa'ilin da Rasha ta ba da goyon bayan sojojinta ga Siriya.
Ya zuwa yanzu dai yakin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 500,000 tare da raunata dubbai tare da lalata sassa da dama cikin kasar.
Yakin ya kuma raba kusan rabin al'ummar Siriya miliyan 23, ciki har da mutane fiye da miliyan 5 da ke gudun hijira a wajen Siriya.