"Muna tsaye ƙyam tare da Turkiyya da al'ummarta a yaƙin da suke yi da ƙungiyar PKK kuma za mu ci gaba da kasancewa haka," in ji Amurka. Hoto: AP

Ma'aikatar Tsaro ta Amurka ta ce ƙasar na jaddada goyon bayanta ga ƙawarta ta ƙungiyar NATO wato Turkiyya da al'ummarta akan yaƙin da take yi da ƙungiyar ta'addanci ta PKK.

Da yake wani jawabi a ranar Litinin, kwana guda bayan da ƙungiyar PKK ta yi ƙoƙarin kai wani harin ta'addanci a Ankara, mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaron Amurkan Matthew Miller ya tuna yadda tun can a baya Amurka ta ayyana PKK a matsayin ƙungiyar ta'addanci ta ƙasashen waje.

"Muna matuƙar goyon bayan Turkiyya da al'ummarta a yaƙin da suke yi da ƙungiyar PKK kuma za mu ci gaba da kasancewa da hakan," a cewar Miller, yayin da yake amsa wata tambaya da wakilin kamfanin dillancin labaran Turkiyya na Anadolu ya yi masa a kan goyon bayan Amurka ga YPG/PKK.

Miller ya jaddada cewa Amurka ta yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai babban birnin Turkiyya Ankara, tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan "samun sauƙi da gaggawa."

"Mun fahimci irin barazanar tsaron da PKK ke zame wa Turkiyya," ya ƙara da cewa.

Ma'aikatar Tsaron Turkiyya ta tabbatar da alaƙar ɗaya daga cikin maharan wanda aka kashe da ƙungiyar PKK, tana mai cewa ana ci gaba da yin bincike kan ɗaya ɗan ta'addar da ya kai harin ranar Lahadin.

Maharan sun ƙwace motar wani ɗan ƙasar Turkiyya ne mai suna Mikail Bozlagan wanda likitan dabbobi ne, suka kai harin da ita, a cewar Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida.

An ji wa wasu ƴan sanda biyu rauni kaɗan a lokacin da ɗaya daga cikin ƴan ta'addan ya tayar da bam ɗin da ke jikinsa a ranar Lahadi da safe a gaban Hukumar Tsaro da ke Ankara.

TRT World