Harin jirgi maras matuki na Amurka ne ya kashe Qasem Soleimani a 2020. / Hoto: Reuters

Akalla mutum 103 aka kashe a Iran bayan wasu abubuwa sun fashe sau biyu a cikin taron wasu mutane wadanda suke tunawa da kisan Janar Qasem Soleimani wanda aka kashe a 2020.

“Akalla mutum 103 suka rasa rayukansu a wannan lamari” wanda ya faru a ranar Laraba a kusa da kabarin shugaban dakarun juyin juya hali na Iran a wani masallaci da ke kudancin birnin Kerman, kamar yadda gidan talabijin na kasar ya ruwaito.

Kafar watsa labarai ta Nournews ta ce “tukwanen gas da dama sun fashe a hanyar zuwa makabartar”.

An ruwaito jami’in kasar yana cewa “babu tabbaci kan ko tukwanen gas ne ko harin ta’addanci ne”.

Kafar watsa labarai ta ta nuna masu ceto na kungiyar bayar da agaji ta Red Crescent suna taimaka wa wadanda suka samu raunin.

Tun da farko an soma ruwaito mutum 20 suka mutu, sai dai daga baya adadin ya yi ta karuwa.

“Kungiyoyinmu na kai agajin gaggawa suna kwashe wadanda suka ji rauni... Sai dai akwai dumbin mutane wadanda suka toshe hanya,” in ji Reza Fallah, shugaban kungiyar Red Crescent reshen lardin Kerman.

TRT World