"Wadannan abubuwa da Isra'ia ke yi na lalala dukkan kokarin da ake yi na kawo zaman lafiya a Siriya da kuma kara ta'azzara wutar rikicin yankin," in ji ma'aikatar. / Photo: AA

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi suka da babbar murya kan yadda Isra'ila ke fadada mamayar yankin Tsaunukan Golan, wadanda tun 1967 Isra'ilan ta mamayi yankin.

A wata sanarwa, ma'aikatar ta kira matakin da "sabon matakin manufar Isra'ila ta fadada iyakokinta ta hanyar mamaya," inda ta bayyana damuwa kan illar da wannan mataki ka iya janyowa.

Sakon sukar na Isra'ila ya yi karin haske kan abubuwan baya bayan nan da ake yi a yankin, ciki har da sabawa Yarjejeniyar Barin Wajen ta 1974 ta hanyar shiga yankin, zuwa ga iyakokin daya tsallaken da kai hare-hare ta sama a Siriya.

"Wadannan abubuwa da Isra'ia ke yi na lalala dukkan kokarin da ake yi na kawo zaman lafiya a Siriya da kuma kara ta'azzara wutar rikicin yankin," in ji ma'aikatar.

Sanarwar ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya kamata wajen magance ci gaba da saba dokoki da Isra'ila ke yi tare da dakatar da matakan da suka karya doka da gwamnatin Netanyahu ta dauka.

Kalaman na Turkiyya na bayyana damuwar kasashen duniya kan manufofin Isra'ila a Tsaunukan Golan, waje mai muhimmanci da ake ta tababa a kai tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da wasu hukumomin kasa da kasa ko kasashe.

TRT World