Ministocin Harkokin Kasashen Waje na kasashen yankin Gulf da ke taro a Jiddah tare da takwarorinsu na Masar da Iraki da Jordan, sun tattauna batun yakin Siriya da kuma yiwuwar mayar da kasar cikin Kungiyar Kasashen Larabawa, amma ba a kai ga daukar mataki ba tukunna, a cewar wata sanarwa daga Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyya.
Sai dai kuma jami'an diflomasiyyar Kasashen Larabawan sun amince cewa dole ne yankin ya tashi tsaye kokarin kawo mafita ga rikicin Siriyan, kamar yadda ma'aikatar Saudiyyan ta fada a ranar Asabar da safe.
Jami'an diflomasiyyar kasashen "sun tattauna kan muhimmancin samar da jagorancin Kasashen Larabawa wajen kawo karshen rikicin," in ji sanarwar.
Wasu Kasashen Larabawa da suka hada da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa sun kyautata alakarsu da Siriya wadda ta lalace tun a 2011 lokacin da Kasashen Yammacin Duniya da wasu na Larabawa da dama suka kaurace wa shugaban Siriya Bashar al Assad, saboda matakan da ya dauka na dakile masu zanga-zanga.
Sai dai har yanzu batun sasantawa da Siriyar da Kasashen Larabawan wani lamari ne da kasashe da dama ba sa son tabo shi.
A farkon makon nan ne Firaministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, ya ce har yanzu ba a janye babban dalilin da ya sa aka dakatar da Siriyan daga zama mamba ta Kungiyar Larabawan a 2011 ba.
Yakin basasar Siriya ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 500,000 tare da tursasawa kusan rabin al'ummar kasar na kafin a fara yaki rabuwa da muhallansu.
A ranar Laraba, a wata alama ta baya-bayan nan da ke nuna kawo sauki ga lamarin da Damascus, Ministan Harkokin Wajen Siriya Faisal Mekdad ya isa Jiddah, a ziyara ta farko tun bayan da aka fara yaki a kasar.
Mekdad da takwaransa na Saudiyya sun tattauna "kan matakai na gaba da suka kamata a dauka" wajen kawo karshen wariyar da ake nuna wa Damascus, kamar yadda wata sanarwa ta Saudiyya ta fada a ranar Laraba.
Daga Saudiyya, Minista Mekdad zai wuce ziyara zuwa Aljeriya ne.
Iran da yakin Yemen
Duk wata shawara kan mayar da Siriya cikin Kungiyar Kasashen Larabawan mai mambobi 22 ka iya zama maudu'in da za a tattauna a kai a taron kungiyar na gaba, wanda za a yi shi a Saudiyya a watan Mayu.
Taron na Jiddah na daga cikin abubuwan mamakin da suka biyo bayan yarjejeniyar da Saudiyya da Iran suka cimma ranar 10 ga watan Maris a China, kan sasantawa tsakanin su, bayan shekara bakwai ana zaman doya da manja.
Haka kuma a ranar Juma'a, an yi musayar kusan fursunoni 900 na yakin basasar Yemen, tsakanin 'yan tawayen Houthi da Iran ke goyon baya da kuma gamayyar rundunar hadakan da Saudiyya ke jagoranta, a lokacin da jiragen da ke dauke da fursunonin suka dinga sintiri tsakanin yankunan da ke karkashin ikon 'yan tawayen da na gwamnati.
A wannan makon ne jakadan Saudiyya a Yemen ya tattauna da dakarun Houthi da nufin kawo karshen mummunan yakin basasar da ake yi tun lokacin da dakarun da Saudiyya ke jagoranta suka shiga tsakani a 2015.