An hango makaman da Iran ta haeba suna wucewa ta saman birnin Ƙudus inda suka nufi cikin Isra'ila./ Hoto: Reuters

Iran ta ƙaddamar da hare-hare a Isra'ila ranar Asabar da tsakar dare, inda ta harba jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami fiye da 200.

Iran ta kai waɗannan hare-haren ramuwar gayya ne bayan Isra'ila ta kai hari a ofishin jakadancinta da ke Syria, inda ta kashe zaratan sojojinta bakwai ciki har da masu muƙamin janar.

Jirage marasa matuƙa da makamai masu linzamin da Iran ta harba su ne karon farko da take kai hari Isra'ila kai-tsaye daga cikin ƙasarta.

Waɗannan hare-hare sun jawo fargaba game da yiwuwar ramuwa daga Isra'ila kan Iran lamarin da zai ƙara zaman ɗar-ɗar ɗin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kafafen watsa labarai sun ruwaito cewa wasu daga cikin makaman da Iran ta harba sun sauka a filin jirgin saman Ramon da ke yankin Negev na Isra'ila.

"Makamai masu linzami samfurin Kheibar sun yi nasarar sauka a sansanin jiragen sama mafi muhimmanci na Negev," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Iran IRNA ya ruwaito, yana mai ƙarawa da cewa "hotuna da bayanai sun nuna cewa harin ya yi wa wurin gagarumar ɓarna."

Rundunar sojojin Isra'ila ta ce Iran ta harba jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami fiye da 200 a ƙasarsu, inda ta bayyana cewa ta kakkaɓo da dama daga cikinsu a kan iyakar ƙasar amma ana ci gaba da gumurzu.

Sai dai ta ce ta "tare" kashi 99 na makaman da Iran ta harba mata.

"An daƙile harin da Iran ta kawo," a cewar kakakin rundunar sojin Isra'ila Rear Admiral Daniel Hagari a saƙon da ya karanta a gidan talbijin.

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alƙawarin bai wa Isra'ila "kariya mai ƙarfin gaske" bayan ya gudanar da taron gaggawa da manyan jami'an tsaronsa kan harin da Iran ta kai wa Isra'ila.

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi tir da harin da Iran ta kai Isra'ila sannan ya yi kira a yi taka-tsantsan tare da daina tayar da jijiyoyin wuya.

A nata ɓangaren, Saudiyya ta nuna matuƙar damuwa game da yadda ake zaman ɗar-ɗar a yankin da kuma tasirin da hakan zai yi, kamar yadda ta faɗa a wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar.

TRT World