Kifar da Bashar Al Asad da kawo sauyin shugabanci a Syria cikin makonni biyu bayan tunkarar babban birnin kasar da 'yan adawa suka yi daga yankunan Idlib da Daraa, ya girgiza jama'a da dama.
An kifar da Assad bayan yakin basasa na shekaru 13. Amma hakan ya zo ne bayan gwagwarmayar da aka fara shekaru 100 da suka gabata.
A lokacin bikin murnar cika shekaru biyar da fara boren Syria a 2016, masu sharhi na muhawarar cewa boren bai yi nasara ba.
Bazarar Larabawan ta koma zuwa Sanyin Larabawa. Kuma Syria ta zama waje mai ruwan sanyi da ba a samu sauyin da ake so ba.
Yadda batutuwan juyin juya hali ke sauya wa na tirsasa mu tunani sama da kallon yankin kawai, wanda dole a kalli yadda masu ruwa da tsaki na yankin da ma duniya baki daya ke taka rawa a yankin.
Game da 'yan adawar Syria, tafiya sannu-sannun 'yan adawar ce ta kawo wannan nasara.
A shekaru masu zuwa ne za a yi warwara da nazari sosai kan juyin juya halin Syria na ranar 8 ga Disamba, musamman ma dga bangarori daban-daban.
Idan muna da sa'a, za mu ji ta bakin dukkan bangarorin da ke da ruwa da tsaki kan yadda aka samu naarar juyin juya halin.
Sai dai kuma, akwai wani abu da ya kamata a fahimta ya zuwa yanzu: dole ne a yi nazari kan juyin juya halin Syria a matsayin abinda aka faro tun 2011, amma kuma wanda yake da alaka da bore da aka yi wa 'yan mulkin mallakar Faransa a 1925 a kasar.
Juyin juya hali wani tsari ne, ba wai taro ba ne. Juyin juya hali na wanzuwa a zamaninnika daban-daban inda wasu mutanen ke koyo daga kwarewar wasu jama'ar da suka gabace su.
Juyin juya hali na da idanuwa, kunnuwa da zuciya. A yayin da aka shirya yin sa, zai iya kama kowa ya dabaibaye shi. Wannan ne abin da ya faru a Syria.
Zamanin juyin juya hali
Wannan na iya zama kamar wani kwarmato, amma tsarin siyasar zamani a duniya na yau bai taba shaida wani sauyi kamar irin wanda ya afku a Syria ba.
E, kifar da gwamnatin Assad ya biyo bayan Boren Larabawa da ya isa zuwa Sham a 2011 tare da direwa a 2024.
Sai dai kuma, ba za a iya kwatanta wannan da irin sauyin shugabanci cikin gaggawa da aka samu a wasu yankunan duniya da zanga-zanga ta janyo, kamar Tunisa da Masar.
Zine El bidine ben Ali ya shugabanci Tunisia tsakanin 1987 da 2011. Hosni Mubarak ya yi shugabanci tsakanin 1981 da 2011.
Shugabancin ben Ali ya kawo karshe bayan kwanaki 28 na boren jama'a. Mubarak ya sauka bayan kwanaki 18 ana yi masa tawaye a kasar.
Kira ga sauyi a koyaushe ya zama iri guda, mai sauki amma dawwamamme, a shekaru 100 da suka gabata, daga 1915 zuwa 2025.
A lokacin da guguwar boren kasahen Larabawa ta isa zuwa Sham a 2011, har a wannan lokacin ana tuna wa da yunkurin baya da aka yi na kifar da dan kama karya.
Wannan ya fito karara bayan an karya kofofin gidan kurkukun Sadnaya a watan da ya gabata.
Misali: matukin jigin sama dan kasar Syria Ragheed Al-Tatari, wanda aka daure yna da shekaru 27 a 1980 saboda ya bijirewa umarnin rundunar sojin kasar na harba bam kan fararen hula a Hama ya kubuta bayan shekaru 43.
Wadanda suka kirkiri juyin juya halin Syria sun fito daga al'adu, sana'o'i d agaruruwa daban-daban.
Kira ga sauyi ya zama iri guda, mai sauki kuma dawwamamme, a shekaru 100 da suka gabata, daga 1925 zuwa 2025.
A lokacin da 'yan Syria suka yi bore ga tsarin Turawan mulkin mallaka na Faransa, taken da aka dinga yi a lokacin shi ne: 'Yanci, Daidaito da 'Yan uwantaka.
A kwanakin farko na fara boren Syria, an dinga rera taken "Assad ko Mu Kona Kasar." Tabbas, wannan ne batun bayan shekaru 13, watanni takwas, da kwanaki 23.
Duk da rikicin siyasar Libya da Yemen, za mu iya cewa, Boren Kasashen Larabawa ya zo karshe da kifar da Bashar Al Assad.
Sabuwar gwamnatin Syria na kokarin sake fasalin siyasa, tattalin arziki da ayyukan soji na kasar daga sama har kasa, wanda ba abu ne mai sauki ba.
A takaicen takaicewa dai, dole ne mutum ya yarda cewa tun bayan kafa kasar Syria ke fama da rikici a koyaushe.
A tsakanin 1922 da 1970, misali, an samu sauyin gwamnatoci har 16, bakwai daga ciki juyin mulkin soji ne.
Kafin iyalan Assad su hau mulki, mafi yawancin shugabannin ba sa wuce watanni 18 a kan mulki.
Dauwamammen juyin juya hali
A yayin da za a ce an kawo karshen Boren Larabawa, amma rikicin Gabas ta Tsakiya na ci gaba.
Bayan shekara guda da rabi Isra'ila na aikata kisan kiyashi a Gaza, juyin juya halin Syria na tuna mana cewa akwai yiwuwar samun sauyin siyasa.
Shin kifar da Assad za ta kawo Boren Larabawa na 2? Wannan tambaya ce mai kyau. Amma a kalla a yanzu, manufofin sabuwar gwamnatin Syria na bayyana ba ta da niyyar "isar" da boren zuwa wasu kasashen yankin.
Juyin juya hali na kira ga manyan bukatu da kare mutuncin dan adam.
Kamar tsarin yin bore ne ga tsohon tsarin da ke kokarin mayar da hankali kan kwakwalen jama'a ko makiya na gida da na waje, kuma maimakon a mayar da hankali wajen rubuta ingantaccen tarihi nasu na kansu.
Syria din Assad biyu ce misali irin wannan. Da yake magana a wajen Taron Hadin Gwiwa na Kasashen Larabawa makonni uku kafin kifar da gwamnatinsa, Bashar Al-Assad bai yi shayin bayyana Syria a matsayin mai kare martabar Falasdinawa ba.
A yayin da a gefe guda, mahaifinsa Hafez ne ya taimaka wajen tarwatsa ayyukan tirjiyar Falasdinawa ta hanyar harar kokarinta a Lebanon.
Tabbas, a yayin da Jumhuriyar Syria ta samu 'yancin kanta bayan janyewar sojojin Faransa gaba daya a ranar 17 ga watan Afrilun 1946, jama'ar Syria sun samu 'yancin kai na gaskiya bayan Bashar Al-Assad ya gudu daga Sam zuwa Moscow.