Daga Omar Abdel-Razek
Shekarar 2024 za ta shaida fadadar kawancen kasashen BRICS inda za a amince da shigar kasashen Habasha da Iran da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, kari kan mambobinta na yanzu (Rasha, Barazil, China, India, Afirka ta Kudu). Ajantina ma ta shirya shiga kawancen a watan Janairu amma kuma sai ta janye.
Wannan ne karo na farko da kawancen ya samu karin mambobi da yawa a lokaci guda, tun bayan sa Afirka ta Kudu ta shiga a 2010. Wannan yunkuri ya kara yawan mambibin kungiyar zuwa 11, inda suke wakiltar kashi 43 na yawan jama'ar duniya, kuma kaso 16 na kasuwancin da ake yi a duniya baki daya.
BRICS, na nufin Barazil, Rasha, Indiya, China da Afirka ta Kudu, kuma Jim O’Neil ne ya fara kirkirar sunan BRIC, a 2001 ba tare da Afirka ta Kudu ba.
Wannan sabon shafi da aka bude, na kawo damarmarki da kuma fargaba. Fata mai kyau da ake da shi shi ne na samun sauyin da aka yi wanda zai habaka tattalin arzikin kasashen masu tasowa, wanda a yanzu suka zama kasuwannin sayar da kayayyakin kasashen da suka ci gaba da zama kasashen da bashi ya yi wa katutu.
Karfafa karfin ikon Afirka
Yadda kawancen ya ki aiki da takunkumin da kasashen Yamma suka saka wa Rasha a yayin da ta fara yaki da Yukren, suka zabi a tattauna, inda suka kuma ci gaba da kasuwanci da Moscow, na nufin hadin kan siyasa da biyan bukatar tattalin arziki.
Shigar da Masar - daya daga cikin kasashe mafi karfin tattalin arziki a Afirka, da Ethiopia, helkwatar Tarayyar Afirka, na kara karfin nahiyar da ke tattare da kawancen. Wannan yunkuri na kalubalantar kasantuwar Afirka ta Kudu a kawancen a matsayin na je ka na yi ka, saboda kasancewar ta kasa mafi kankanta a tsakanin kasashen.
Shigar Ajantina, da ya zama mai wakiltar Latin Amurka a kawancen.
A duniyar da ke sadarwa da juna a yau, yadda ba za ka iya raba siyasa da tattalin arziki ba, na wajabtawa BRICS ta habaka da samun karfin fada a ji a fagen siyasar duniya, musamman duba da nasarar da China da Rasha suka samu.
Wani batu mai matukar muhimmanci game da wannan tafiya shi ne samar da sabon tsarin ci gaba a duniya da yake kalubalantar na Yammacin duniya, misali shi ne nasarar da Sabon Bankin Cigaba (NDB) ya kawo, wanda ya amince da bayar da dala biliyan $32.8 don gudanar da manyan ayyuka a kasashe.
Sabon tsarin biyan kudade
Ana yi wa NDB kallon shi ne amsar sabon tsarin da "kudancin duniya" don kalubalantar matakan da IMF da Yarjejeniyar Washington suka kawo. Shawarar da Rasha da China suka kawo na samar da sabon tsarin biyan kudade na kasa da kasa, na kalubalantar Dalar Amurka, wanda ake bai wa kasashen BRICS gudanar da kasuwanci a tsakaninsu ta hanyar amfani da kudadensu, inda hakan zai saukakawa kasashen Afirka wajen samun saukin bashin da ake bin su.
Masar, da take maraba da karbar ta a kawancen, na tsammanin samun raguwar bukatar kudaden kasashen waje ta hanyar manufar rage amfani da dala da kawancen kasashen ke da shi.
Ethiopia, da take daga cikin kasashen Afirka da ke habaka cikin gaggawa, na son irin wannan alfanu da zai iya sanya kasar daina fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya kan batutuwa irin su 'hakokin dan adam'.
An yi amanna cewa wannan yunkuri zai habaka suna da karfin Ethiopa a duniya, zai kara kusantar da kasar ga mu'amala da manyan kasashe, da kuma sauya labarai game da kasar daga rikicin da aka yi kwanan nan, ta yadda za a ja hankalin masu zuba jari zuwa kasar.
Sai dai kuma, a yayin da wannan fata nagari, akwai kula kalubalen da ka iya zuwa. Tarihin irin wannan yunkuri na bayyana hadin kai da kudu maso-kudancin duniya ke yi, na kokarin jirkitawa da maye gurbin tsarin da ya mammaye ko'ina da Yammacin duniya ya kawo. Yunkuri na farko shi ne gwagwarmayar rabuwa da 'yan mulkin mallaka.
A 1995, Bandung ya karbi Babban Taron Asia-Afirka na farko, taron da shugaban kasar Indonesia Sukarno ya bayyana a matsayin "babban taron kasa da kasa na farko tsakanin mutane masu kala a tarihin dan adam".
Amma kuma, tsarin da duniya ke kai bai wani sauya abubuwa da yawa ba, kuma mamayar Yammacin duniya ta hanyar hukumomin kudi na kasa da kasa da manyan kamfanunnuka na ci gaba.
Bambance-Bambance da tsaka mai wuya
A yayin da ba lallai BRICS su kawo wata barazana nan da nan ga kawancen G7 ko G20 ba, saboda manufar kungiyar ta dogare ne kan magance mamayar da dalar Amurka ta yi a fagen kasuwancin duniya, wanda hakan na kalubalantar Amurka, kuma za ta ji tsoron habakar kasashen", in ji mai nazari kan kan tattalin arzikin Afirka ta Kudu Marisa Lourenco.
Kalubale a tsakanin kawancen kansa, tun daga batun karfin tattalin arziki tsakanin China da India, wadanda su ne a yau suke matsayin kasashe na biyu da na biyar mafiya tattalin arziki, da kuma kasashen d abashi ya yi wa katutu irin su Masar da Ethiopia.
Batutuwan siyasa kamar rikicin kan iyaka tsakanin Chinda India, takaddama kan kogin Nil tsakanin Masar da Ethiopia, da adawar yankin Gulf tsakanin Saudiyya da Iran, na bayyana irin tsaka mai wuyar da BRICS ke ciki bayan kara yawan mambobin da kungiyar ta yi.
Fasali da zubin BRICS ya ishi kawancen ya ci ribar damarmakin bambance-bambancen da ke tsakanin su, ba tare da dakatar da ayyukan ci gaba ba. Kawancen ya dogara kan gudanar da taron shekara-shekara, a yayin da tarukan zartar da hukunce-hukunce suke kasancewa ba tare da wasu sharudda ko waje na musamman ba.
Ya rage a gwada yadda hadin kai tsakanin kasashe zai kasance ba tare da cusguna wa wani bangare ba, a lokacin da ake gogayya tsakanin Amurka da kawayenta a gefe guda, a dayan gefe kuma ake da China da nata kawayen.
Marubucin, Omar Abdel-Razek, masanin zamantakewar dan adam ne, tsohon editan BBC Arabic. Yana aiki da zama a birnin Landan.
Togaciya: Ba lallai ra'ayin da marubucin ya bayyana ya zama ya yi dai-dai da ra'ayi ko manufofi na TRT Afirka ba.