Netanyahu zai kauce wa Turai a hanyarsa ta zuwa Amurka don gudun kama shi / Hoto: AA / Photo: Reuters

1103 GMT –– Netanyahu zai kauce wa Turai a hanyarsa ta zuwa Amurka don gudun kama shi

Rahotanni sun ce Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu yana duba yiwuwar kauce wa shiga Turai a kan hanyarsa ta zuwa Amurka saboda ya guje wa yiwuwar kama shi, a cewar kafar watsa labaran ƙasar Isra’ila ta KAN.

Wannan shawarar na da nasaba da fargabar cewa kasashen Turai za su iya tilasta wa kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) sammacin kama Netanyahu kan yiwuwar sa hannu a laifukan yaki da kisan kiyashi a Gaza na Falasdinu.

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, wanda yanzu ke cikin kwanaki 278, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa aƙalla 38,243 - akasarinsu mata da yara -- ya kuma raunata 88,033 sannan ana hasashen cewa aƙalla sama da mutum 10,000 ke binne a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine da 9,500 da suka rushe.

Sama da watanni tara da yakin da Isra'ila ke ci gaba da gwabzawa a zirin Gaza, manyan yankunan yankin sun kasance kango a cikin wani gurguntaccen shingen hana samun abinci, ruwan sha da magunguna.

Ana tuhumar Isra'ila da aikata kisan kiyashi a kotun kasa da kasa, hukuncin da ta yanke na baya-bayan nan ya umurci Tel Aviv da ta gaggauta dakatar da aikin soji a kudancin birnin Rafah, inda kafin mamayar Isra'ila, sama da Falasdinawa miliyan guda suke neman mafaka daga yaƙin a wajen.

1103 GMT –– Rundunar sojin Isra'ila ta umarci dukkan mazauna Birnin Gaza su fice daga cikinsa sannan su tafi birnin Deir al-Balah da ke tsakiyar yankin.

Rundunar sojin ta riƙa watsa wasu takardu ɗauke da sanarwa ga mazauna Birnin Gaza su fice daga cikinsa nan-take sannan su nufi biranen Zawaida da Deir al-Balah.

“Birnin Gaza zai kasance wuri mai hatsari na ba-ta-kashi,” in ji saƙon da ke cikin takardun.

Kazalika saƙon ya nuna hanyoyin da mutane za su bi domin ficewa daga Birnin Gaza ba tare da fuskantar hatsari ba, inda aka umarce su da su bi ta hanyar Salah a-Din ko kuma yankunan gaɓar teku.

0625 GMT –– Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 8 cikinsu har da yara 6 a Gaza

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla takwas a wani hari ta sama da ta kai da daddare a wasu gidaje a tsakiyar Gaza a a yayin da ta shiga kwana na 278 tana luguden wuta a yankin, kamar yadda kafafen watsa labaran yankin suka ruwaito.

Kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa na Wafa ya ce Isra'ila ta kashe Falasɗinawa takwas, ciki har da yara shida, sannan ta jikkata mutane da dama a hare-hare ta sama da ta kai agidajensu a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat.

Kazalika dakarun Isra'ila sun yi luguden wuta a yankuna daban-daban na Gaza, ciki har da harin da ta kai a gidajen da ke Titin Naser a arewacin Birnin Gaza da ya jikkata aƙalla mutum 10.

Kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa na Wafa ya ce Isra'ila ta kashe Falasɗinawa takwas, ciki har da yara shida, sannan ta jikkata mutane da dama a hare-hare ta sama da ta kai agidajensu a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat. / Hoto: AA

I0111 GMT ––Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 29 a harin da ta kai a wata makaranta a Gaza; ta sa an rufe asibitoci

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 29 a harin da ta kai ta sama a wata makaranta da 'yan gudun hijira suke samun mafaka a kudancin Gaza ranar Talata, a yayin da luguden wutar da dakatunta suke ci gaba yi a arewaci ya sa aka rufe asibitocin Birnin Gaza tare da tilasta wa mutane tserewa daga gidajensu domin neman mafaka.

Sojojin Isra'ila sun yi kisan kiyashi a makarantar Al-Awda da ke garin Abasan na gabashin Khan Younis, a cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza ta fitar.

Galibin yankunan Birnin Gaza sun kasance tamkar kufayi sakamakon luguden wutar da dakarun Isra'ila suka kwashe watanni tara suna yi a yankin. Yawancin mutanen da ke birnin sun tsere tun da aka fara yaƙin, amma dubban mutane na ci gaba da zama a arewaci.

A watanni tara da Isra'ila ta kwashe tana yaƙi a Gaza, dakarunta sun mamaye asibitoci aƙalla takwas, inda suka kashe majinyata da ma'aikatan kiwon lafiya tare da lalata gine-gine da kayan aiki.

Isra'ila ta yi zargin cewa ƙungiyar Hamas tana mafani da asibitocin ne domin ajiye makamai, ko da yake ba ta bayar da cikakkun shaidu game da zargin nata ba.

Asibitoci 13 daga cikin 36 da ke Gaza ne suke aiki a halin yanzu, kuma su ɗin ba ba sa aiki kamar yadda ya kamata, a cewar ofishin jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya.

An kai Falasɗinawa Asibitin Al-Aqsa Martyr domin yin jinya bayan Isra'ila ta kai musu hari a yankin Deir al-Balah / Hoto: AA

2239 GMT — Fadar White House ta zargi Iran da amfani da abin da ke faruwa a Amurka saboda rikicin Gaza don shisshigi cikin lamuran ƙasar, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, bayan wani gargaɗi da wani babban jami'in tattara bayanan sirri na Amurka ya yi cewa Iran na son rura wutar yanayin da ake ciki a Amurka.

Gargaɗin, wanda Daraktan Hukumar Leƙen Asirin ƙasar Avril Haines ya yi, ya ce wasu mutane dake da alaƙa da gwamnatin Iran da suke bayyana kansu a matsayin farar-hula ne a shafukan sada zumunta, suna yunƙurin ƙarfafa gwiwar masu zanga-zanga, har suna ba su kuɗaɗe.

Kakakin Fadar White House Karine Jean-Pierre ta ce 'yancin faɗin albarkacin baki na da muhimmanci ga dimokuraɗiyyar Amurka, sai dai gwamnati na da alhakin gargaɗin 'yan ƙasarta kan tasirin wasu daga ƙasashen waje.

"Amurkawa daga kowane ɓangare da suke aiki da zuciya ɗaya, suna ƙoƙarin bayyana ra'ayinsu na ƙashin kansu kan rikicin Gaza. Idan aka yi amfani da 'yancin bayyana ra'ayoyi mabambanta cikin lumana hakan abu ne mai muhimmanci ga dimokraɗiyyarmu," kamar yadda ta bayyana,

"A lokaci guda kuma, gwamnatin Amurka na da alhakin gargaɗin Amurkawa dangane da mummunan tasiri daga waje... Za mu ci gana da tona asirin duk wani yunƙuri na yi wa dimokuradiyyarmu ƙafar-ungulu kamar yadda muke yi a yau.

An kai Falasɗinawan da aka jikkata ciki har da yara, Asibitn Shahidan na Al-Aqsa bayan harin Isra'ila a yankin Deir al-Balah . / Hoto: AA
TRT World