Falasɗinawa suna ƙoƙarin ci-gaba da rayuwarsu ta yau da kullum a cikin ɓaraguzan gine-ginen da aka ruguza a hare-haren da Isara’ila ta ke kaiwa a Gaza. / Hoto: AA

Isra’ila ta amince da shirin janye sojoji daga Gaza, bayan samun ci-gaba a tattaunawar musayar fursunoni da Hamas, a cewar kafofin watsa labarai.

Jaridar Haaretz ta ce hukumomin soji sun amince da shirye-shirye da dama na janye sojoji daga Gaza nan take, saboda ci-gaban da aka samu a tattaunawa.

Ta duba zaɓin da ake da su, da suka haɗa da janye sojoji daga zirin Netzarim, wanda ya raba Gaza gida biyu.

Duk da cewa ta kafa muhimman abubuwa da kuma jibge dakaru a wurare a yankin, rundunar sojan ta ce za ta iya “janye” dakarunta, inda ta jaddada kasancewarta a shirye ta aiwatar da duk wata yarjejeniya da aka cim ma tsakanin gwamnati da ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa, ciki har da gagarumin janye dakaru daga Gaza.

Tun da farko ofishin Firaministan Isra’ila ya bayyana cewa wata tawaga ƙarƙashin shugaban Hukumar Leƙen Asirin Ƙassar Mossad, David Barnea da Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri da Tsaro ta Shin Bet internal security service Ronen Bar za ta tafi Qatar don ci-gaba da tattaunawa.

Gabanin sanarwar, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gana da Steve Witkoff – jakada na musamman a Gabas ta Tsakiya ga Shugaban Amurka mai jiran Gado Donald Trump.

Ita ma jaridar Yedioth ta rawaito ce, an kammala 90% na tsarin yadda za a yi musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas, inda jaridar take ambato majiyoyi na siyasa.

‘Mummunan’ yaƙi

Kawo yanzu, babu wata sanarwa a hukumance da fito daga Hamas, ko kuma ƙasashen da suke shiga tsakani, Masar da Qatar da Amurka da ta tabbatar da cim ma yarjejeniyar.

Sai dai mai wani magana da yawun ƙungiyar Hamas Jihad Taha ya shaida wa gidan talabijin na Al-Jadeeda a ranar Asabar cewa Hamas ta amince da tsarin tsagaita wutar, kuma ma har an kammala tsara daftarin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, abin da ake jira kawai shi ne amincewar Isra’ila.

Fiye da Falasɗinawa 46,537 ne suka rasa rayukansu, fiye da 109,378 suka jikkata a yaƙin da Isra’ila take yi a Gaza tsawon kwanaki 464, kamar yadda alƙaluman hukumomin lafiya na Gaza suka nuna.

To sai dai wani bincike mai zaman kansa da masana daga jami’ar London School of Hygiene & Tropical Medicine (LSHTM) suka gudanar ya ce, ana rage adadin mutunen da suka mutu a hare-haren Isra’ila a Gaza da kimanin kaso 41, inda aka kashe kashi uku cikin ɗari na jama’ar yankin a yaƙin da ake yi.

Binciken ya ƙiyasta cewa mutanen da suka mutu saboda hare-haren a Gaza sun kai 64,260 daga 7 ga Oktoban 2023 zuwa 30 ga Yulin 2024, idan aka kwatanta da 37,877 da Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ba da rahoto.

Sakamakon binciken, wanda aka wallafa a mujallar lafiya ta The Lancet a ranar Juma’a, ya nuna cewa aƙalla kashi uku na mutanen Gaza sun mutu sakamakon yaƙin, inda wasu alƙaluman suka nuna cewa kaso 59 daga cikinsu mata ne da yara da tsofaffi.

TRT World