Ana rage adadin mutunen da suka mutu a hare-haren Isra’ila a Gaza da kimanin kaso 41, inda aka kashe kashi uku cikin ɗari na jama’ar yankin a yaƙin da ake yi, a cewar wani sabon bincike.
Wani bincike mai zaman kansa da masana daga jami’ar London School of Hygiene & Tropical Medicine (LSHTM) suka gudanar, ya ƙiyasta cewa mutanen da suka mutu saboda hare-haren a Gaza sun kai 64,260 daga 7 ga Oktoban 2023 zuwa 30 ga Yulin 2024, idan aka kwatanta da 37,877 da Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ba da rahoto.
Sakamakon binciken, wanda aka wallafa a mujallar lafiya ta The Lancet a ranar Juma’a, ya nuna cewa aƙalla kashi uku na mutanen Gaza sun mutu sakamakon yaƙin, inda wasu alƙaluman suka nuna cewa kaso 59 daga cikinsu mata ne da yara da tsofaffi.
Masu binciken sun yi amfani da wata hanyar tattara alƙaluma da lisaffin da aka fi sani da "capture-recapture analysis" wajen ƙiyasin adadin mutanen da suka mutu saboda hare-haren, yayin da alƙaluman ɗakin ajiye gawawwaki na asibitin da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Lafiya, da bincike ta hanyar amsa tambayoyi ta intanet, da ta’aziyyar da ake yi a shafukan sa da zumunta suka kasnce hanyoyin da aka bi wajen tattara alƙaluman.
Binciken ya gano cewa, yawan mutanen da suka mutu zuwa Oktoban 2024 ya haura 70,000, wanda a lokacin ma’aikatar lafiya ta ce kimanin 42,000 aka kashe.
Sakamakon ya jaddada ɗaukar matakin gaggawa wajen shiga tsakani don tsare fararen hula da dakatar da ƙarin rasa rayuka,” a cewar Zeina Jamaluddine wacce ta jagoranci wallafa binciken na LSHTM.
Isra’ila ta ci gaba da yaƙinta na ƙare dangi a Gaza tun bayan harin da Hamas ta kai ranar 7 ga Oktoban 2023, duk kuwa da ƙudirin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da yake kira a tsagaita wuta nan take.
Ci gaba da kashe-kashen zuwa shekara ta biyu ya janyo mummunar suka a duka faɗin duniya, inda jami’ai da cibiyoyi suke bayyyana hare-haren da hana shigar da kayan agaji a matsayin wani yunƙuri da gangan na rusa wata jama’a.
A watan Nuwamban 2024, Kotun Duniya Kan Hukunta Manyan Laifuka (ICC) ta ba da sammacin kama Firaminista Benjamin Netanyahu da tsohon Ministan Tsaro Yoav Gallant saboda laifukan yaƙi da cin zarafin bil’adama a Gaza.
Isra’ila tana kuma fuskantar wata shari’ar a Kotun Duniya kan kisan ƙare dangi saboda mummunan yaƙin da take yi a Gaza.