Alhamis, 14 ga Nuwamban 2024
1844 GMT –– Jakadan Amurka a Lebanon ya miƙa wani daftari na shirin tsagaita wuta ga kakakin majalisar wakilan Lebanon Nabih Berri don dakatar da yaƙi tsakanin Hezbollah da Isra'ila, kamar yadda wasu majiyoyi biyu na siyasa suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, ba tare da ƙarin bayani kan abin da ya ƙunsa ba.
Amurka ta sha yunƙurin tsara yarjejeniyar tsagaita wuta da za ta kawo ƙarshen yaƙin da ake yi tsakanin ƙawarta Isra'ila da Hezbollah, amma duk yunkurin ba su kai ga cim ma nasara ba.
1845 GMT –– Amurka ta nuna 'damuwa' kan hare-haren Isra'ila a unguwannin bayan garin Beirut
Amurka ta bayyana damuwa bayan ƙawarta Isra'ila ta kai hari kan wuraren da ta yi zargin cewa na Hezbollah ne a unguwannin bayan garin Beirut, tana cewa tana adawa da hare-hare a wurare masu cunkoson jama'a a Lebanon.
"Tabbas muna damuwa," a cewar mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Vedant Patel lokacin da aka tambaye shi dangane da hare-haren na Isra'ila.
"Kun ji mu mun sha faɗa cewa ba ma son ganin irin wannan aikin (na soja) a Beirut, musamman ma idan suka danganci wuraren da jama'a da dama ke zaune."
1238 GMT –– Akalla mutane 15 ne suka mutu kana wasu 16 suka jikkata a hare-haren da Isra’ila ta kai kan wasu gine-ginen gidaje da ke wajen birnin Damascus na kasar Siriya, kamar yadda kafafen yada labarai na gwamnatin ƙasar suka rawaito.
Gine-ginen gidajen na cikin yankunan Mazzeh da Qudsaya waɗanda ke yammacin babban birnin ƙasar, a cewar rahoton Kamfanin dillancin labaran Siriya SANA.
Gidan rediyon sojojin Isra'ila ya ce wuraren da aka kai harin a Damascus, hedkwatar ƙungiyar Islamic Jihad ta Falasdinu ne da kuma wasu muhimman wurare, sai dai bai wani yi ƙarin haske akai ba.
Karin bayani 👇
1358 GMT –– Isra'ila ta kusa cim ma yarjejeniya kan Lebanon: Minista
Ministan tsaron Isra'ila ya bayyana cewa, Isra'ila tana gab da cim ma matsaya kan faɗan da ake yi a Lebanon.
"Ina ganin mun kai wata matsaya da ba mu taba kai wa ba na cim ma yarjejeniya tun da aka fara yakin," in ji ministan makamashi Eli Cohen a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi da shi.
1226 GMT –– Rahotannin farko kan harin da Isra'ila ta kai a yankin Damascus na Mazzeh
Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Siriya ne ya fara fitar da labarin farko kan harin da Isra'ila ta kai yankin Mazzeh da ke wajen birnin Damascus.
1223 GMT–– Isra'ila ta kai harin kusan maki 30 cikin sa'o'i 48 a kudancin Beirut
Dakarun Isra'ila sun ce sun kai hare-hare kusan maki 30 a yankunan kudancin birnin Beirut bayan sa'o'i 48 da suka wuce.
1159 GMT –– Iran ta shaida wa babban jami'in makaman nukiliya na MDD cewa ba za ta yi zaman shawarwari karkashin yanayin' tsoratarwa' ba.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, ƙasarsa ba za ta yi zaman shawarwari karkashin yanayin “tsoratarwa” ba, a yayin wata tattaunawa mai cike da ruɗani da babban jami’in makaman nukiliya na MDD suka gudanar, makonni kafin zababben shugaban Amurka Donald Trump ya hau mulki.
Shugaban Hukumar Makaman Nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya ce samun "sakamako" a tattaunawar nukiliyar da Iran na da matukar muhimmanci don kaucewa barkewar wani sabon rikici a yankin da tuni yakin Isra'ila ya tarwatsa a Gaza da Lebanon.
Ziyarar tasa ta biyo bayan wasu 'yan kwanaki da ministan tsaron Isra'ila, Isra'ila Katz ya ce, Iran ''ta fi fuskantar hare-hare kan cibiyoyinta na nukiliya,'' inda hakan ya baiwa Isra'ila ''damar cimma burinmu mafi muhimmanci.''
Grossi ya ce bai kamata a ''kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran'' ba, amma ana sa ran Trump zai baiwa Isra'ila damammaki masu yawa bayan ya hau mulki a watan Janairu.
1139 GMT – Isra’ila ta kama wasu Falasdinawa 6, 'yan kama -wuri-zauna sun kai hari kan manoma
Sojojin Isra'ila sun kama wasu Falasdinawa 6 a wani samame da sojoji suka kai a yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye a daidai lokacin da 'yan kama-wuri-zauna na Isra'ila ke kai sabbin hare-hare kan manoman Falasdinawa.
Dakarun sojin Isra'ila sun kai samame a wasu garuruwan da ke gabar yammacin kogin Jordan, da suka hada da Nablus, da Jenin, da Tubas, da Ramallah, da kuma Bethlehem, a cewar wata sanarwa ta haɗin gwiwa da hukumar kula da harkokin da kungiyar fursunonin Falasdinawa suka fitar.
Kamfanin dillancin labaran Falasdinu na WAFA ya ce an kai samame kan gidaje da dama a yayin farmakin.
A garin Bani Naim da ke gabashin Hebron, sojojin Isra'ila sun kai samame gidaje da dama tare da tsare wasu matasa su tara da kuma yi musu tambayoyi kafin su sake su, inji WAFA.
1114 GMT–– Hanyoyin yakin Isra'ila 'sun dace da kisan ƙare dangi' in ji Kwamitin MDD
Hanyoyin yakin Isra'ila a Gaza sun yi daidai da kisan ƙare dangi, ciki har da fararen hula wadanda aka kashe tare da azabtar da Falasdinawa da gangan, a cewar wani Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya na Musamman.
1022 GMT — Isra'ila ta fitar da rahoton hare-haren rokoki da na jirage marasa matuka daga Lebanon da Iraki
Isra'ila ta fitar da rahoton harɓin rokoki da jirage marasa matuka daga kasashen Lebanon, da Iraki da kuma Siriya a daidai lokacin da rikicin yankin ke ci gaba da ta'azzara sakamakon yakin da ta ke yi a Gaza.
0735 GMT — An kai hari kudancin Beirut bayan umarnin kwashe mutane na Isra'ila - Rahoto
Wani hari ta sama da Isra'ila ta kai ya afka wa yankunan kudancin babban birnin kasar Labanon bayan da Isra'ila ta gargadi mazauna yankin da su fice daga wani bangare na sansanin Hezbollah, kamar yadda hotunan AFP suka nuna.
Wani hayaki mai launin toka ya turnuƙe yankin bayan harin na baya-bayan nan tun bayan da Isra'ila ta tsananta kai hare-haren bam a Lebanon a watan Satumba.
Jim kadan gabanin harin, Isra’ila ta yi gargadi ga mazauna yankin da su bar gidajensu.
0745 GMT — Isra'ila ta kai harin bam a birnin Gaza, inda ta kashe Falasdinawa da dama
Harin bama-bamai da Isra'ila ta kai a unguwar Sheikh Radwan da ke birnin Gaza inda fararen hula ke zaune, ya kashe Falasdinawa akalla uku.
A wani hari na daban da aka kai a wajen makarantar Hamama, Isra'ila ta raunata Falasdinawa 10, in ji cibiyar yada labarai ta Falasdinu (PIC).
Har ila yau Isra'ila ta tsananta kai hare-hare a duk fadin Gaza, inda aka harba makaman atilari a yankunan kudanci da gabashin unguwar Zeitoun.