Kamfanin dillancin labaran kasar Falasdinu, Wafa, ya fitar da rahoton cewa, "Sojojin mamayar sun harbe Abu Saan a kai". / Hoto: AFP

Daruruwan mutane ne suka halarci jana'izar wani matashin Bafalasdine da sojojin Isra'ila suka kashe a yammacin gabar Kogin Jordan da suka mamaye.

A wata sanarwa da ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta fitar a ranar Juma’a, ta ce an kashe Mahmoud Abu Saan mai shekaru 18 ''a safiyar ranar ta hanyar harbinsa da harsashi kai-tsaye daga mamayar (Isra'ila) a Tulkarm.''

An lullube gawar Abu Saan da tutar Falasdinu yayin da aka zagaya da ita a kan titunan garin gabanin binne shi, a cewar wani mai daukar hoto na kamfanin dillacin labaran Faransa AFP.

An lullube gawar Abu Saan da tutar Falasdinu, a cewar wani mai daukar hoto na AFP.

Da farko dai, kamfanin dillancin labaran Falasdinu Wafa ya ce "dakarun mamaya ne suka harbi matashin a kai a wani harin kusa da suka kai."

Lamarin ya faru ne a lokacin da sojojin Isra'ila suka kutsa cikin sansanin 'yan gudun hijira na Tulkarem tare da harba bindigogi da barkonon-tsohuwa kan Falasdinawa mazauna wurin.

Tashin hankalin da aka alakanta da rikicin Isra'ila da Falasdinu a bana ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 206 da 'yan Isra'ila 27, a cewar wata kididdiga da kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar.

TRT World