Hamed Safi, daga dama, mamban tawagar Afganistran, na magana da abokin aikinsa a yayin taron COP29 a Baku, a ranar 11 ga Nuwamba, 2024, ranar da aka fara taron sauyin yanayi na MDD na 2024. / Photo: AFP

Gwamnatin Taliban ta halarci taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a karon farko tun bayan karbar ragamar Afghanistan a 2021, in ji hukumar kula da muhalli ta kasar.

An fara gudanar da taron na COP29 a ranar Litinin a Azabaijan, kuma daya daga cikin muhimman tattaunawa da za a yi shi ne kan Taliban.

Ana sa ran sun sami matsayin 'yan kallo a wajen taron.

Hukumar Kula da Kare Muhalli ta Kasa ta sanar ta shafinta na X cewa jami'anta sun halarci taron da ake gudanarwa a Baku.

Matiul Haq Khalis, shugaban hukumar, ya ce tawagar za ta yi amfani da taron wajen karfafa hadin kai da kasashen duniya kan kare muhalli da rikicin sauyin yanayi, sannan za su bayyana bukatar Afganistan na samun damar amfani da kudadenta na sauyin yanayi, sannan su tattauna kan kokarin rage tasiri.

Tasiri kan Afghanistan

Kwararru sun fada wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa rikicin sauyin yanayi ya janyo illoli da dama kan Afganistan, ya kawo kalubale manya saboda yankin da kasar take da rashin daukar kwararar matakan yaki da illar.

"Rikicin sauyin yanayi ya janyo dumamar yanayi, wanda ke rage ruwan da ake samu don amfani, tare da janyo fari, wanda ke illata harkokin noma" in ji Hayatullah Mashwani, farfesa kan kimiyyar yanayi da muhalli a Jami'ar Kabul.

"Raguwar ruwan da ake da shi da yawaitar fari na yi babbar barazana ga ayyukan noma, wanda ke kawo karancin abinci da kalubalen ji dadin rayuwa."

A watan Agusta, kungiyar agaji ta kasa da kasa 'Save The Children' ta fitar da wani rahoto da ke cewa Afganistan ce kasa ta shida a duniya mafi rauni da ke illatuwa da tasirin sauyin yanayi, kuma 25 daga lardunanta 34 na fuskantar matsanancin fari, wanda ke shafar sama da rabin jama'ar kasar.

Afganistan kuma na da yara mafi yawan yara da illar sauyin yanayi ya raba da matsugunansu ya zuwa karshen 2023.

Farfesa Abid Arabzai, na Jami'ar Kabul ya ce taron na sauyin yanayi zai taimaka wajen samun tallafin kasa da kasa da kudade don magance kalubalen sauyin yanayi a Afganistan.

"Afganistan na iya fayyace matakai da kokarin da take yi na yaki da sauyin yanayi ga kasashen duniya,tana sake inganta darajarta a matakin kasa da kasa," in ji Arabzai.

TRT World
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince