Daga FAYHA SHALASH
Rana ce kamar kowacce rana a rayuwar iyalan Malalha da suka fito daga kauyen Bazariya na kusa da Nablus a Yammacin Gabar Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye, amma a cikin dan kankanin lokaci komai ya sauya.
A ranar 23 ga Yuni, Akram Malalha na tuka mota zuwa kasuwa tare da dansa dan shekara biyar, mai suna Khaled.
A yayin da suke wucewa ta babban titin garin, sai suka ji karar harbe-harbe a wata mashigar kauyen - ashe rikici ake yi tsakanin mazauna yankin da sojojin Isra'ila.
Akram bai kula da cewa harsashi ya samu idon dan karamin dansa da ke zaune a kujerar baya ba. Har sai bayan Khaled ya fara rusa kuka da ihu. Mahaifin ya waiwaya inda ya ga fuskar dansa sharkaf da jini.
Akram ya shaida wa TRT World cewa "Lamari ne mummuna. Jini ya baibaye fuska da tufafin Khaled. Ban san ashe alburushi ne ya daki idonsa ba.
Nan da nan na tsayar da motar na je kujerar baya don rarrashin sa. A sannan ne na ga wata babbar huda a jikin gilashin motata, sai na fahimci lallai harsashin da sojojin Isra'ila suka harba ne ya hudo ya same shi."
A wajen iyalin da ma karamin yaron, awannin da suka biyo baya sun zama na bakin ciki, sun kai yaron wani asibiti da ke kusa, sannan aka mayar da shi zuwa Asibitin An-Najah da ke garin Nablus, inda a nan ma likitoci suka ce ba su da kayan aikin da za su duba idon.
A wannan dare, an kai yaron wanda ya riga ya jikkata zuwa Asibitin Hadassah da ke Birnin Kudus, inda likitoci suka bai wa mahaifin mummunan labarin cewa sai dai a cire idon gaba daya don kubutar da rayuwarsa.
Mahaifin ya kara da cewa "Mun zama kamar wasu masu nutsewa da ke fafutukar kubuta, muna ta tunanin me za mu yi don kar Khaled ya rasa idonsa. Amma abun ya zama ya munana ta yadda ba makawa sai dai a cire idon."
Saboda hatsari da wahalar da ke tattare da tiyatar da za a yi masa, an mayar da Khaled zuwa Asibitin Tel Hashomer da ke Tel Aviv. Ya yi nasarar samun kulawa ba tare da jinkiri ba.
Hanyar kai Falasdinawa asibitocin isra'ila na da matukar wahala a yanzu. Akwai Falasdinawa da yawa da suke ta zaman jira a kai su asibiti a Isra'ila, inda suke zaman jira na tsawon lokaci, kwanaki, makonni ko ma watanni kafin su samu a mayar da su can.
Ana yawan sukar asibitocin Isra'ila saboda gallaza wa Falasdinawa marasa lafiya, kuma suna kokarin nuna wa duniya su ba sa nuna bambanci wajen gudanar da ayyukansu, ba sa nuna wariya ga marasa lafiya da ba Falasdinawa ba.
A yawancin lokuta, Falasdinawa da suka samu raunuka na fuskantar matsaloli irin na rashin amincewar jami'an tsaro hana su zuwa asibitocin Isra'ila.
Mazauna Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye na shan wahala sosai saboda dokokin da aka saka kafin mutum ya je asibitin Isra'ila.
Dokar kasa da kasa ta tanadi cewa isra'ila da ta zama shugabar mamaya, dole ta dauki alhakin tabbatar da kula da lafiya da walwalar Falasdinawa.
Wannan ya hada da bayar da damar samun kula da lafiya da tabbatar da sun samu magunguna da ci gaba da kula da su a ko yaushe. Isra'ila za ta samar da yanayin tabbatar da an kai kayan kula da lafiya da magunguna idan Bafalasdine ba shi da lafiya.
Game da batun Khaled, an cire idonsa a Asibitin Tel hashhomer, an saka wata farar kwalba a madadin idon. Yarin ya fuskanci matsananci zafi lokacin tiyatar da bayan an gama.
Amma babbar illar da aka smau ta shafi kwakwalwa - abun da har yanzu ke damun Khaled. A kowacce rana, yana sa mahaifinsa zubar da hawaye a duk lokacin da ya tambayi "Ina son idona ya dawo. Yaushe likitoci za su dawo min da idona?
Akram ya ja dogon numfashi tare da cewa "Yana tambayar ina idonsa yake, ya kuma san sojojin isra'ila ne suka raba shi da shi, amma yana fatan zai dawo."
Wannan yanayi da ya shiga na kara tabarbarewa sakamakon yadda Khaled ya ki bayar da goyon baya ga likitan kwakwalwa. Maimakon haka, sai ya ware kansa. Ba ya son yin wasa, ba ya son ya hau mota tare da babansa.
Da gangan
Kungiya Mai Zaman Kanta ta Kare Yara Kanana da ke Geneva ta bayyana cewa ya zuwa yanzu Falasdinawa hudu sun rasa idanuwansu a wannan shekarar saboda harbin bindiga daga Isra'ila.
Tariq Jama Jumaa mai shekara 15 ya zama wanda aka kai wa hari na baya-bayan nan, wanda ibtila'in ya same shi a ranar 12 ga Agusta.
Daraktan tabbatar da gaskiya a kungiyar, Ayed Abu Qutaishi ya shaida wa TRT World cewa da gangan sojojin Isra'ila ke kai hari kan Falasdinawa fararen hula da suka hada da yara kanana, inda ake harbin su a fuska ko wani bangaren saman jikinsu, wanda hakan ke janyo musu nakasa ta dindindin.
Kungiyar ta kuma ce daga farkon shekarar nan alburusan Isra'ila sun kashe yara kanana Falasdinawa 40, inda a 2022 suka kashe yara 44. Sun kuma yi ikirarin cewa ba wai harar idanuwa ne manufar sojojin isra'ila ba, kawai harin ne manufarsu.
Abu Qutaish ya ce Isra'ila na amfani da kariyar da take samu daga kasashen duniya, wanda hakan ke sanya ake zuba wa sojojinta idanu suna yadda suka ga dama.
Kotun Hukunta Manyan laifuka ta Duniya da ke Rome ta tanadi cewa wadannan abubuwa sun fado karkashin laifukan yaki na kashe dan adam."
Bayan yaran sun rasa idanuwansu su da iyayensu na shiga mawuyanci hali na damuwa da kunar zuci, duk da akwai kungiyoyin da ke bayar da taimakon sanyaya zuciya, amma raunin na dauwama a tattare da su.
Abu Qutaish ya kara da cewa "Nufar yaran Falasdinawa ba shi da iyaka. Ya hada da harbinsu, bin su da gudu, kama su, azabtar da su bayan kama su, kuma ba abun da Isra'ila ke fuskanta sakamakon wannan mummunan abu."
"Ina ji na ban cika ba"
A ranar 24 ga Afrilu, Omar Assi mai shekara 16 ya kasance a harabar gidansu a lokacin da sojojin Isra'ila suka harba gurneti zuwa rufin kwanon gidan. Gurnetin ya fado a gabansa tare da fashewa da kuma jikkata shi a fuska.
Nan da nan, sai duniya ta yi masa duhu, ba ya iya ganin komai. Ya yi ihu a yayin da jini ke fita daga fuskarsa. An kai shi asibiti cikin gaggawa, inda suka yi kokarin yi masa magani.
"Bayan awanni a dakin tiyata, likitoci sun fito sun fada wa iyalansa cewa ya rasa idonsa guda daya, kuma suna ta kokarin kubutar da dayan," in ji Omar.
Fashewar gurnetin da ya taba fuska da kansa ya yi muni sosai. Tsawon kwanaki ya dauka ba tare da iya bude idonsa ba, kuma bai ma san saura kadan ya rasa idanuwan nasa gaba daya ba.
Ya ce "A lokacin da na bude idanuwana, ban ga komai ba a bangaren idon dama. A bangaren hagu kuma, na ga hazo da dishi-dishin motsin mutane a tare da ni. Bayan haka, na sake fuskantar tiyata har sau hudu a idon hagu, babu wanda ya kara karfin gani na."
Bayan wannan ciwo, rayuwar Omar ta sauya gaba daya. Bai iya kammala zangon karshe a makaranta ba saboda rashin gani.
Sai ya kusanto da abu kusa da idanunsa kafin ya gane mene ne. Yana zaune a gida ko yaushe, ba ya son fita waje tare da abokansa ko mahaifinsa kamar yadda yake yi a baya.
"Ina jin kaskanci. Ina son rayuwata ta koma kamar ta da, na yi karatu, na dinga yawo da abokaina na taimaki iyayena. Isra'ila ta hana ni dukkan wadannan abubuwa," in ji Omar.
Mahaifin Omar, Talal Asi ya bayyana mana yadda dukkan rayuwarsu ta sauya. Ba za su iya barin Omar shi kadai ba saboda yana da wata leda a idonsa, ba a so a dinga motsa shi sosai. Sun yi kokarin tallafa masa da dukkan bukatarsa ta yau da kullum.
Ya ce "Omar ne babban dana, shi ne kashin bayan gidan nan, saboda kuzarinsa, yana kai kawo don taimaka mana. Yana da raha a ko yaushe. Amma yanzu yana cike da bakin ciki da damuwa."
Rashin tausayi
Ba wai yara kanana kawai isra'ila ke nufa ba wajen harbi. Nufar idanuwan Falasdinawa ya zama al'adar sojojin Isra'ila a lokacin da ake fafata rikici.
Kungiyar Bayar da Agaji ta Falasdinu ta bayyana cewa wasu mazauna kauyen Bita su shida, a kudancin Nablus, sun gamu da harbi a idanuwansu a yayin rikici kan filaye da Yahudawa a shekarar da ta gabata.
An jikkata Falasdinawa 12 a Birnin Kudus a tsakanin shekarar 2021 da 2022, inda aka harbe su a idanuwansu a yayin rikici ya barke a garin.
Issa Amro, wani mai fafutuka da ke Falasdinu, yana adawa da kama guri zauna da mamayar da Yahudawa ke yi, ya bayyana cewa Isra'ila na nufar saman gangar jikin yara kanana musamman ma idanuwansu, saboda dalilai da dama.
Babban dalilin shi ne su azabtar da Falasdinawa da suke ci gaba da nuna musu tirjiya.
Amro yana ganin sojojin Isra'ila a matsayin masu tsaurin ra'ayi da nuna wariya, wadanda ke kokarin azabtar da yaran Falasdinawa.
Ya kara da cewa "An yi nasara kan sojan Isra'ila, shi ya sa yake ganin zamansa zai tabbata ta hanyar zalunta da nufar yara kanana Falasdinawa da makamai."