Israel's Iron Dome anti-missile system operates, amid hostilities between Hezbollah and Israeli forces. / Photo: Reuters Archive

Laraba, 13 ga Nuwamban 2024

1442 GMT — Hezbollah ta ce ta kaddamar da wani harin jirgin sama mara matuki kan hedkwatar sojojin Isra'ila da ma'aikatar tsaro a birnin Tel Aviv.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta Lebanon ta ce ta kai wani harin ta sama tare da tawagar jiragen sama marasa matuƙa masu fashewa a wurin da ke da manyan cibiyoyin tsaron Isra'ila a cibiyar kasuwanci.

1217 GMT — Adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya haura 43,700 yayin da hare-haren Isra'ila ke ƙara tsananta

Akalla karin Falasdinawa 47 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu tun bara zuwa 43,712, in ji Ma’aikatar Lafiya a yankin.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa an jikkata wasu 103,258 a harin da ake ci gaba da kai wa.

Ma'aikatar ta ce: "A mamayar da Isra'ila ta yi, ta yi wa iyalai bakwai kisan kiyashi cikin sa'o'i 24 da suka wuce, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 47 da jikkata 182."

0714 GMT — Harin da Isra'ila ta kai wani gida a kudancin Beirut ya kashe mutum 8

Harin sama da Isra'ila ta kai kan wani gida ya kashe aƙalla mutum takwas a unguwar Dawhet Aramoun da ke kudancin Lebanon, a cewar kamfanin dillancin labarai na ƙasar.

Sannan harin wanda aka kai unguwar Dawhet Aramoun ya jikkata mutane da dama, kamar yadda NNA ya rawaito.

Rahotanni sun ce harin ya kuma lalata gine-gine da dama.

0655 GMT –– Dakarun Isra'ila sun kai hari a Lebanon da sanyin safiya

Dakarun Isra'ila sun kai hari a gidajen jama'a a unguwar Dawhet Aramoun da ke kudancin birnin Beirut, a cewar kafofin watsa labaran ƙasar.

Kamfanin dillancin labarai na National News Agency ya ruwaito cewa jiragen yaƙin Isra'ila sun kai harin ne da sanyin safiyar, inda suka jikkata jama'a.

Za mu kawo ƙarin bayani nan gaba kaɗan...

2327 GMT —Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 7 a kudancin Gaza

Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla bakwai tare da raunata wasu da dama a hare-haren da ta kai ta sama a Gaza da ta yi wa ƙawanya.

Sojojin Isra'ila sun kai hari kan wata rumfa da ke gefen titi da ake sayar da kayayyaki a yankin Qizan Abu Rashwan da ke kudancin Khan Younis, inda suka kashe Falasdinawa biyu tare da jikkata wasu da dama, kamar yadda shaidun gani da ido suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

A wani harin da Isra'ila ta sake kai wa, wata majiyar lafiya ta shaida wa Anadolu cewa Falasdinawa uku ne suka mutu, wasu goma kuma suka jikkata, yawancinsu kananan yara, a wani harin da aka kai ta sama a wani gida da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza.

A cewar majiyar, daya daga cikin wadanda suka jikkata ya rasu kafin a isa Asibitin Al-Awda da ke Nuseirat, yayin da wasu goma suka samu raunuka.

An kai wasu “sassan jikin” mutum biyu da abin ya shafa asibitin shahidan Al-Aqsa, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana.

A cewar majiyar, daya daga cikin wadanda suka jikkata ya rasu kafin a isa Asibitin Al-Awda da ke Nuseirat / Photo: AA

Ƙarin bayani 👇

2315 GMT — Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da 2,000 a arewacin Gaza cikin kwana 38

Ofishin yada labarai na yankin Gaza ya ce Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 2,000 a arewacin Gaza cikin kwana 38.

Daraktan ofishin Ismail al-Thawabta ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa hare-haren sun yi illa ga mata da yara da kuma tsofaffi.

Al-Thawabta ya yi kira ga kasashen duniya da su shiga tsakani cikin gaggawa, yana mai yin Allah wadai da matakin da Isra'ila ta dauka a matsayin wani gangamin kisan ƙare dangi ga Falasdinawa a Gaza, musamman a arewacin kasar.

Ya danganta alhakin rikicin jin ƙai ga kasashen Amurka, Birtaniya da Turai, yana mai zarginsu da hannu a manufofin "yunwa da kashe-kashen jama'a."

TRT World