Baya ga tsananin zafi da ke addabarta, kasar Bahrain a yanzu kuma tana fama da wata babbar barazanar ta muhalli: tumbatsar teku da ka iya hadiye wasu sassanta, a cewar ministan muhalli na kasar.
Kasar wacce take yankin Gulf za ta fara gina wata katanga a gabar tekunta don kare ta daga barazanar tumbatsar teku da ke tunkararta, ta hanyar fadada gabobin tekun da gina doguwar katanga.
"Bahrain na cikin hatsari," a cewar Mohamed bin Mubarak bin Daina, ministan man fetur da muhalli kuma jakada na musamman kan harkokin sauyin yanayi na Bahrain, a wata hira da aka yi da shi.
"Babbar barazanar barazana ce mai tunkararmu a hankali, wato ta tumbatsar teku," ya fada a ofishinsa da ke babban birnin kasar Manama.
Kiyasin hukumomi ya nuna cewa, tumbatsar da tekun ke yi da kafa 16.4 zai hadiye mafi yawan sassan kasar, ciki har da babban filin jirgin samanta.
Ko da da mita 0.5 tekun ya tumbatsa to zai iya shafe kashi 18 cikin 100 na Bahrain, in ji Sabah Aljenaid, wani mataimakin farfesa a Jami'ar Manama ta kasar.
Bahrain ce kawai kasar da ke kan tsibiri a cikin kasashen yankin Gulf masu arzikin man fetur. Mafi yawan al'ummarta da manyan wurarenta suna yankin gabar teku ne kasa da mita bakwai da inda ruwa yake.
Sauran tsibiran da ke fadin duniya ma na fuskantar barazanar tumbatsar teku yayin da dumamar yanayi ke narkar da kankara.
'Katangar dutse'
Hukumomin Bahrain tuni suka ce torokon da ruwan tekun yake yana tsakanin mililita 1,6 zuwa mililita 3,4 duk shekara tun 1976, a cewar bin Daina.
Amma nan da shekarar 2050, yawan ruwan teku zai karu da a kalla mita 0.5, kamar yadda ministan ya fada.
Cikar teku na kara ta'azzara ambaliyar ruwa da barazana ga gabar teku, kuma yana iya gurbata matattarar ruwan karkashin kasa na Bahrain da ruwan gishiri.
Bin Daina ya ce "Hakan ya sanya daya daga cikin abubuwan da Bahrain ta bai wa fifiko shi ne tumbatsar teku."
"Ko dai mu fadada gabar teku da ake wanka da shakatawa, ko mu gina katangar dutse a wasu wuraren, ko kuma karbe kasar da kusa da gabar tekun."
Wani bangare ne na "bayyanannen tsari" da za a kammala "a cikin shekaru 10" kuma gwamnati za ta dauki nauyinsa, kamar yadda ministan ya bayyana.
Kasar da Shirin Sabo da Duniya na Notre Dame ya bayyana a matsayin daya daga kasashen yankin Gulf ga suke da rauni da fuskantar barazanar sauyin yanayi, dole ne Bahrain ta yi la'akari da yanayin zafi mai cutarwa a daya daga cikin yankuna mafiya zafi a ban kasa.
Kwararru na gargadin cewa nan da karshen wannan karnin, tsananin zafi da sauyin yanayi yake janyo wa na iya hana zama a yankin Gulf.
Tuni Bahrain ta fara shan wannan zafi.
Wannan watan, an samu kafa tarihin zafi wanda ya kai daraja 44 a ma'aunin salshiyas, wanda ke sanya a kure na'urar sanyaya daki.
Taka rawa biyu
"A dukkan shekarun da suka gabata, ba a samu amfani da lantarki kamar a wannan shekarar ba, saboda zafin na kara yawa," in ji bin Daina.
A kokarin ayyukanta na yaki da sauyin yanayi, Bahrain, karamar kasa mai samar da man fetur mara yawa, na shirin rage fitar da hayaki da kashi 30 nan da 2035, sannan za ta habaka makamashinta mai sabuntuwa da kashi 10 nan da wannan lokaci.
Tana kuma duba yiwuwar ribanya yankunan da suke da bishiyoyi koraye da suka ninka bishiyoyin mangroves sau hudu, wadanda su ne za su zuke iskar carbon a cikin shekara 12.
Bin Daina ya ce ba ya ganin sabani a rawar da yake takawa a matsayinsa na ministan mai da muhalli - abu wanda aka saba gani a kasar ta yankin Gulf,
Mahukuntan kula da muhalli na Kuwait na karkashin ma'aikatar man fetur, kuma Hadaddiyar Daular Larabawa ta zabi Sultan Al Jaber, wanda ke shugabantar kamfanin ADNOC a matsayin shugaban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP28 da za a gudanar a Dubai.
Bin Diana ya ci gaba da cewa "Samun mutum guda na kula da ma'aikatun muhalli da man fetur a lokaci guda, na nufin yadda Bahrain ta mayar da hankali wajen yaki da sauyin yanayi."
Ministan "Zai iya sanya dukkan dokoki a masana'antun mai", in ji shi, inda ya yi watsi da cewar ayyukan hydrocarbon na iya lalata yanayi.