Harin sama na Isra'ila ya kashe aƙalla mutum biyar a yankin Baalshmay na Bairut. /Hoto: Reuters Archive

Talata, 12 ga Nuwamban 2024

1408 GMT Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon ta ce wani harin da Isra'ila ta kai ya kashe mutane biyar a tsaunukan gabashin Beirut bayan wani jami'in tsaro ya ce an kai hari wani gida da 'yan gudun hijira ke samun mafaka.

A wani rahoton farko da ma'aikatar ta fitar ta ce, harin da maƙiya Isra'ila suka kai kan Baalshmay ya kashe mutane biyar.

Jami'in tsaron da yake magana ba tare da bayyana sunansa ba saboda tsaro, ya ce harin na Isra'ila ya faɗa kan wani gidan da 'yan gudun hijirar ke zaune ciki har da mata da yara.

A yau ne Isra'ila ta kai hare-hare ta fiye da 10 a kudancin Beirut, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta bayyana, jim kadan bayan da sojojin Isra'ila suka gargadi jama'a a unguwanni da dama da su fice daga cibiyar Hezbollah.

0821 GMT — An gina 'ramin tsaro' a babban birnin Iran bayan harin da Isra'ila ta kai

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya bayar da rahoton cewa, Iran na gina wasu "ramin tsaro" a Tehran babban birnin kasar, biyo bayan harin da Isra'ila ta kai kan wasu yankuna a kasar.

Ramin wanda ke kusa da tsakiyar birnin, zai hada tashar da ke tashar jirgin kasa ta Tehran da asibitin Imam Khumaini, ta yadda za a ba da damar shiga karkashin kasa kai tsaye zuwa asibitin.

"A karon farko a kasar, ana gina rami mai dauke da aikace-aikacen kariya a Tehran," in ji shugaban kula da harkokin sufuri na majalisar birnin Tehran ya shaida wa Tasnim.

Ƙarin labarai 👇

0923 GMT — Sojojin Isra'ila sun ba da umarnin kwashe mutane daga wasu unguwanni a kudancin Lebanon

Sojojin Isra'ila sun umurci mazauna unguwanni uku a kudancin Beirut da su fice daga yankunansu gabanin kai hare-hare ta sama.

Sanarwar da sojoji suka fitar ta umurci mazauna yankin da su nisanci mita 500 daga gine-gine da dama a unguwannin Haret Hreik da Ghobeiry da Al-Leik a yankin kudancin Beirut.

A cikin sanarwar, an maƙala taswirar gine-ginen da aka yi niyyar kai wa harin, tana mai cewa za a far wa ƙungiyar Hezbollah “da ƙarfi” a kan abin da ta kira kadarori da muradun ƙungiyar a yankin.

Sojojin Isra'ila sun sha ba da umarnin kwashe fararen hula a yankuna da dama na kasar Lebanon tun bayan fara kai hare-hare ta sama kan kasar a karshen watan Satumba.

0923 GMT — Kungiyoyin agaji sun ce Isra’ila ta gaza biyan bukatun Amurka na kawo saukin bala’in Gaza

Kungiyoyin ba da agaji na ƙasa da ƙasa sun bayyana cewa, Isra'ila ta gaza cim ma jerin buƙatu na Amurka da ke da niyyar inganta ayyukan jin ƙai a Gaza zuwa wa'adin da aka bayar na ranar Talata.

Amurka ta shaida wa ƙawayenta Isra'ila a wata wasiƙa a ranar 13 ga watan Oktoba cewa dole ne ta dauki matakin inganta harkokin agaji cikin kwanaki 30. Idan ba haka ba, tana iya fuskantar yuwuwar hani kan taimakon sojojin Amurka.

"Ba wai kawai Isra'ila ta gaza cika ƙa'idojin Amurka da za su nuna goyon baya ga ayyukan jin kai ba, amma a lokaci guda ta dauki matakan da suka ƙara dagula lamarin a kasa, musamman a arewacin Gaza," in ji wani rukunin kungiyoyin agaji takwas da suka hada da Oxfam da Save the Children da Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Norway ta ce a cikin rahoton mai shafi 19.

TRT World