Sojojin Isra'ila sun harbe wani Bafalasdine a Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, a cewar sanarwar da gidan talabijin na Falasdinu ya fitar.
Mutumin ya mutu ne sakamakon mummunan rauni da ya samu a wani samame da sojoji suka kai garin Zawata da ke yammacin birnin Nablus, da ke arewa maso Gabar Yammacin Kogin Jordan.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce martani dakarunta suka mayar kan harbin da bafasdinen ya yi musu a lokacin da suke gudanar da aikinsu a birnin Nablus, wurin da ya yi kaurin suna wajen yawan kai hare-hare da kuma fafatawa a tsawon watanni 15 da suka gabata.
Sojojin sun ce "suna sane da harin" da aka kai kuma ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta tabbatar da mutuwar mutum guda.
Kungiyar mayakan Al Aqsa ta yi ikirarin cewa mayakin da aka kashe daya daga cikin 'ya'yanta ne.
Kokarin tattaunawa kan zaman lafiya da Amurka ta yi da nufin kafa kasar Falasdinu a Yammacin Kogin Jordan da Gaza da kuma Gabashin Kudus ya ci tura a shekarar 2014 kuma har yanzu babu wata alama da ke nuna cewa tana shirin sake komawa kan batun.
Tashe-tashen hankula da hare-hare sun dada kamari tun a bara a Yammacin Gabar Kogin Jordan, yankin da Isra'ila ta mamaye a yakin 1967 kuma inda Falasdinawa ke da iyakacin ikon mallaka.
Tun daga farkon wannan shekara, yankin ke ci gaba da fuskantar hare-hare da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai wa kan mazauna garuruwan Falasdinawa.