Wani sabon bincike ya nuna cewa fiye da mutane manya miliyan 800 ne suke fama da ciwon suga a faɗin duniya - lamarin da ke nuna yadda yawan ya nunka sau biyu idan aka kwatanta da ƙiyasin da aka taɓa yi a baya - kuma fiye da rabin masu fama da cutar da suka haura shekaru 30 ba sa karɓar magani.
A shekarar 2022, an samu kusan mutum miliyan 828 daga masu shekaru 18 zuwa sama suna fama da nau'i na 1 da na 2 na cutar suga a fadin duniya, kamar yadda binciken da aka wallafa a mujallar lafiya ta The Lancet ya gano. Mutum miliyan 445 daga cikin manya masu shekara 30 zuwa sama ko kashi 59%, ba sa shan magani, in ji mawallafan binciken.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO a baya ta ƙiyasta cewa kusan mutum miliyan 422 ne suke da ciwon suga, wata mummunar cuta da ta haɗa yawan sikari a cikin jini, wadda ka iya illata zuciya da jijiyon jini da sauran sassan jiki idan har ba a ɗauki matakin magance ta ba.
Yawan masu fama da cutar suga a duniya ya nunka sau biyu tun shekarar 1990 daga kusan kashi 7 zuwa 14 cikin 100 kamar yadda binciken ya nuna, wanda ya fi mayar da hankali a kan yadda cutar ke ƙaruwa a ƙasashe matalauta da masu matsakaicin samu.
Amma duk da cewa akwai wasu masu fama da cutar sosai, yanayin kula da lafiya ga masu cutar a waɗancan yankunan ba ya ƙaruwa, in ji mawallafan, yayin da abubuwa kuma suka inganta a ƙasashe masu arziki - lamarin da ya jawo wawakeken giɓi na kula da cutar.
Kashi 5% na masu fama da cutar kawai ke samun magani a Afirka
A wasu sassan Afirka da ke kudu da hamadar Sahara, alal misali, kashi 5-10 cikin 100 na wadanda aka ƙiyasta cewa suna da ciwon suga ne kawai ke samun magani, in ji Jean Claude Mbanya, farfesa a Jami’ar Yaounde I a Kamaru. Yin maganin ciwon sukari, ko dai da insulin ko magunguna, na iya zama tsada.
"Akwai mutane da yawa da ke cikin hadarin kamuwa da munanan matsalolin lafiya," in ji shi.
An yi binciken ne ta hanyar hadin giwa da NCD da WHO, kuma shi ne bincike na farko na duniya wanda ya haɗa da ƙididdigar jiyya ga duk ƙasashe, in ji marubutan. Ya dogara ne a kan fiye da bincike 1,000 da suka shafi mutane fiye da miliyan 140.