Gubar dalma na kashe sama da mutum miliyan biyar a duk shekara: Bincike

Gubar dalma na kashe sama da mutum miliyan biyar a duk shekara: Bincike

Sabon binciken ya bayyana yadda gubar dalma take shafar lafiyar kwakwalwar yara kanana a kasashen Afirka.
Kiyasin binciken ya gano, mutane miliyan 5.5 da suka yi wata mu’alama da gubar ta dalma suka mutu sakamakon ciwon zuciya a shekarar 2019./ Hoto: AP

Gubar dalma na yin mummunar illa ga lafiyar dan adam fiye da yadda ake tunani, domin kuwa sama da mutum miliyan biyar ne suke mutuwa a duk shekara saboda shakar gubar a cewar wani sabon binkice da aka fitar a ranar Talata.

Binciken, wanda aka bayyana shi a matsayin "kira domin farkarwa", ya nuna yadda gubar ke shafar lafiyar kwakwalwar yara kanana a kasashen Afirka da kusan maki shida kan ko wanne yaro.

An gano yadda gubar dalma ke yin mummunar illa ga lafiyar dan adam, musamman wajen haifar da cututtukan da suka shafi zuciya da yanayin ci-gaban kwakwalwar kananan yara, abin da ya sa aka haramta amfani da mai da ake hadawa da dalma a fadin duniya.

Sai dai duk da wannan mataki da aka dauka har yanzu mutane na fuskantar barazana ta illar gubar ta hanyar abinci da ake ci da ire-iren kayayyakin dafa abinci da takin zamani da kayayyakin kwalliya da ruwan baturan mota da karin wasu hanyoyin.

An wallafa sabon binciken da wasu masana tattalin arziki daga Bankin Duniya su biyu suka rubuta a mujallar kiwon lafiya ta Lancet Planetary, inda suka ce binciken shi ne karo na farko da aka tabbatar da tasirin da illar gubar dalma ke da shi ga lafiyar zuciya da lafiyar kwalwalwar yara a kasashen da suka ci-gaba da masu arziki da kuma mace-macen da ake samu.

Jagoran binciken Bjorn Larsen ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa a lokacin da suka fara ganin adadin binciken da suka yi, " ko da wasa ba mi iya gaya wa kowa ba" saboda adadin na da yawan gaske.

Binciken ya gano mutane miliyan 5.5 da suka yi mu’alama da gubar ta dalma sun mutu sakamakon ciwon zuciya a shekarar 2019, kuma kashi 90 daga cikinsu sun fito ne daga kasashe masu karamin karfi da matsakaicin kudin shiga.

Adadin ya ninka wanda aka samu a baya har sau shida, kuma ya kai kusan kashi 30 cikin 100 na dukkan mace-mace da ake samu daga cututtukan da suka shafi zuciya – cuta mafi girma da ke haddasa mutuwa a duniya.

Hakan na nufin an fi kamuwa da ciwon zuciya idan aka yi mu'amala da gubar dalma fiye da shan taba ko abubuwan da ke kara kitse, in ji Larsen.

Binciken ya kuma gano yadda yara 'yan kasa da shekara biyar suka rasa jimillar maki miliyan 765 na basirarsu sakamakon tuamali da gubar dalma a shekarar 2019, kashi 95 cikin dari na adadin da aka samu sun fito ne daga kasashe masu tasowa.

Wannan adadin ya kusa kai wa kashi 80 cikin 100 na kiyasin da aka yi a baya.

Masu binciken daga Bankin Duniya sun ce kudaden da ake kashewa a mu'amala da gubar dalma su kai dala miliyan shida a shekarar 2019, kwatankwacin kashi bakwai na kudaden shiga da ake samu a duniya.

Masu binciken sun yi amfani da wani adadi na jini da ke dauke da gubar daga kasashe 183 da aka samu a binciken da aka yi na 2019 kan manyan cututtuka a duniya.

Binciken da aka yi a baya ya auna tasirin gubar dalma a cututtukan da suka shafi zuciya musamman ga masu fama da matsalar hawan jini.

Sai dai sabon binciken ya yi nazari kan wasu hanyoyin da dama da gubar ke shafar lafiyar zuciya, kamar daskarar jijiyoyin jini da ke haifar da bugun zuciya, a cewar Larsen.

TRT Afrika