Ana yi wa ungulai kallon matsayin jami'an tsaftace duniya. Hoto: M. Froneman

A ko ina kana iya ganin mushensu, gashi da kasusuwansu a barbaje suna wari. A dazukan da dabbobi suke, ganin irin wannan mutuwa na hakaito mana yadda ake farautar dabbobi a dazukan. Amma kuma wadannan mushen ungulaye ne, wadanda watakila da suna nan suna bin su suna caccaka a baya.

Wannan ne abun da ya faru a Gunea-Bissau a 2020, a lokacin da aka saka wa ungulu sama da 2,000 guba; a Bostwana kuma a 2019 an kashe ungulaye 537; in da Namibia a 2013 sama d ungulu 400 suka mutu bayan cin wani mushe mai guba.

Masu rajin kare rayuwar tsuntsaye da sauran dabbobi sun yi korafi kan yadda Afirka ke rasa ungulayenta. Suna ta mutuwa inda suke fuskantar hatsarin karewa baki daya.

Wani rahoto da ‘BirdLife International’ suka fitar ya bayyana cewa daga cikin nau’ikan ungulu 11 da ake da su a nahiyar, guda bakwai suna fuskantar hatsarin karewa gaba daya, kuma wasu hudu na fuskantar barazana.

Idan ungulayen suka kare gaba daya, za a samu yaduwar cututtuka da dama kamar yadda aka gani a Indiya a 1990: Ereson

“Ungulu mai farin baya, wadda ita ce aka fi gani a Afirka, na karewa da kaso 90. Idan aka kalli sauran nau'ika kamar irin ta Masar da ungulan Hood, za a ga sun ragu da kaso 92”, in ji Matsvimbo, jami’in Birdlife International Mai Kula da Ayyukan Hana Dabbobin Karewa, yayin tattauna wa da TRT Afirka.

Kalubalen bayar da kariya

Bayar da guba da kuma farauta ne babban kabulabale ga ungulayen da ke Afirka. Kasancewar su dabbobin da aka fi farautar su, sai suka zama mafiya shan wahala, a wasu lokuta suna fadowa daga bishiyoyi a mace, a wasu lokutan kuma suna gamuwa da cin mushen da aka sanya wa guba wanda ke yin ajalinsu.

A tsawon mil da yawa ana iya hango gungun ungulaye na cin mushe; a mafi yawancin lokuta masu farautar dabbobin dawa na saka musu guba don su mutu ta yadda ba za su sanya jami’ai su gano su ba.

A tsakanin 2012 da 2014 an samu mutuwar ungulaye 2,044 a kasashen Afirka bakwai da ke da alaka da farautar dabbobin dawa, kamar yadda oryx – Mujallar Kasa da Kasa ta Kare Dabbobi ta fada.

Daliba na amfani da wasu sassan jikin ungulu wajen wajen dogaro don cin jarrabawa. Hoto: Sankai

Tsuntsayen suna kuma mutuwa sakamakon gubar da makiyaya suke sanya wa dabbobin dawa da ke cinye musu dabbobi inda tsautsayi sai ya sanya ungulayen su zo su ci naman mai guba.

Haka zalika bukatar ungulu don hada magungunan gargajiya da tsafe-tsafe na daya daga cikin abubuwan da ke karar da ungulaye. Masu ba su kariya na alakanta cewa kaso 29 na karewar ungulu na alaka da hakan.

Kawuna da kwakwalwar ungulaye ne suka fi daraja wajen sayarwa saboda camfin da ke tattare da su ko kuma sun fi amfani wajen yin tsafi.

Ana bayyana cewa dalibai na amfani da su wajen wajen dogaro don cin jarrabawa, kuma masu magungunan gargajiya na amfani da bangarorin ungulu don gana wa da kakanninsu da suka shude, baya da maganin wasu cututtukada suke cewa ungulu na yi.

Bayan lamarin sanya guba ga ungulaye a Guinea-Bissau, a 2020, masu bincike sun gano ‘yan kasuwa na sayar da ungulu da sassanta da aka boye a cikin kahon wasu dabbobin na daban.

Sun gano ana sayar da kan ungulu kan kusan dala 25, kafa kuma dala 15.

Ana sayar da kan ungulu kan kusan dala 25, kafa kuma dala 15. Hoto: J. Onoja

Sannan wani abu da aka bayyana yana kashe ungulaye shi ne rashin wajen zaman su, hawa wayoyin lantarki su mutu, karo da turakun lantarki na iska da hanyoyin makamashi.

A tsakanin 1996 da 2016, tsuntsaye 1,261 sun mutu a lokuta 517 bayan sun hau kan wayoyin makamashin lantarki a Afirka ta Kudu kawai, kamar yadda alkaluman da Asusun Kare Dabboboin Da Ake Wa Barazana ya tattara suka bayyana.

Gungun masu tsaftace muhalli

Ungulaye sun zama wani bangare na tsaftace muhalli kuma suna taka rawa sosai wajen hana yaduwar cututtuka da dama, ba wai kamar abun da ake tunani ba game da cin mushe, suna taimaka wa wajen tsaftace duniya.

Masu ba su kariya na cewa bayan sun ci abinci, suna neman wajen wanka don tsaftace jikinsu.

A lokacin da suka afkawa mushe suna ci, ba wai suna hana yaduwar cututtukan da mushen zai yada ba ne kawai, suna kuma tsaftace rayuwarsu ta dawa daga manyan cututtuka masu yaduwa.

Sinadarin narkar da abinci da suke da shi a cikinsu na daga cikin mafi karfi a duniya wanda ke hana kwayoyin cuta girma.

Ungulaye na iya cin naman da ya gurbata da cututtuka kamar antraks da kwalara da zazzabin dabbobi, kuma ba tare da sun yi rashin lafiya ba, sannan suna hana wadannan cututtuka yaduwa.

A lokacin da wasu dabbobin kamar su kare, mage ko beraye suka ci irin wannan abinci ko nama, za su zama masu yada cututtukan a cikin mutane, idan har sun tsira da rayuwarsu kenan.

Ungulaye na iya rayuwa na tsawon shekaru 30, amma kuma suna dadewa ba su girma ba. Hoto: Derek Keats

Yadda ungulaye suke kare wa abu ne da ya kasance bai damu mutane da dama ba, wasu ma ba sa lura da hakan. Masanan kimiyya na gargadin cewa watsi da batun ungulaye hatsari ne ga rayuwar dan adam.

Matsvimbo na kungiyar BirdLife International ya tunatar da cewa lafiyarmu ta dogara ne kan tsuntsaye da rawar da suke takawa wadda hakan ya sanya ake kiran su da ‘Gungun masu tsaftace duniya’.

Ta ce “Yi tunani, idan aka ce rana guda ba ku kwashe dattin gidanku ba. Idan kana rayuwa a birni, yi tunanin yadda za ta kasance idan mahukunta ba su sanya an kwashe shara ba a kan lokaci, me zai faru?

"Da mun samu cututtuka da dama da doyi da za su yi ta damun mu. Ungulaye na yin irin wannan aiki kyauta. Wadannan tsuntsaye na tashi sama da haka suna yin wannan aiki, suna cinye mushe tare da kare mu daga cututtuka. Me ya sa ba za a kauna ce su ba?”

Idan ungulayen suka kare gaba daya, za a samu yaduwar cututtuka da dama kamar yadda aka gani a Indiya a 1990 lokacin da kusan kaso 97 na tsuntsayen suka mutu.

“Abun da ya faru shi ne suna amfani da maganin diclofenac don yi wa shanu magani, amma ba su sani ba cewa yana illa ga ungulaye idan suka ci mushen shanun.

"Ungulaye da dama sun mutu. Saboda ba a saka ungulaye a lissafi lokacin da shanun suka mutu. Daga baya an samu yaduwar cutar zazzabin dabbobi,” in ji Matsvimbo.

A wasu lokutan ta kara da cewa, babu wanda ya alakanta wannan cuta da rashin wanzuwar ungulayen. A lokacin da aka gano hakan, sai da Indiya ta zuba kudi wajen sake kaddamar da ungulaye a kasar don yaki da cutar.

Ungulai. Hoto: Munir-Virani.

Tare da dimbin bukatu, Matsvimbo ta lura da cewa dawo da ungulai da yawa ba zai zama abun da gwamnatoci za su bai wa fifiko ba.

“Yi tunanin me zai faru, kalli kasashen Afirka, muna bukatar kudade don yin abubuwa da dama, wa ma yake ta batun kara yawan ungulaye. Amma babban abun yi shi ne mu tabbatar da ba mu rasa ungulayen da muke da su ba,” in ji ta.

Ungulaye na iya rayuwa na tsawon shekaru 30, amma kuma suna dadewa ba su girma ba. Masana na cewa ungulaye mace da namiji na haihuwar da daya ne dukkan shekaru biyu.

Yadda ba sa haihuwa da wuri, tare da kuma kalubalen da suke fuskanta na kashewa, na nufin hatsari babba wanda idan ba a dauki matakan da suka kamata ba za su kare baki daya.

Amma kuma akwai fata nigari da ake da shi kan kokarin da ake yi na ganin ungulaye sun ci gaba da yawon cin mushen ba tare da an cutar da su ba.

Matsvimbo ta ci gaba da cewa “A Kudancin Afirka mun samar da yankin rayuwa ba tare da tsangwama ba ga ungulaye mai girman hekta sama da miliyan guda a kasashen Zambia da Zimbabwe da Afirka ta Kudu.”

Ta ce “Kungiyoyin taimaka wa Ungulaye da aka kafa a Zimbabwe na aiki sosai don rage gubar da suke ci.

Kungiyar na aiki da masu magungunan gargajiya a Yammaci da Kudanci da gabashin Afirka don hana kasuwancin sassan jikin ungulu.”

TRT Afrika