Sinadari mai hadari na “toxin” nau’in fungi yana damun tsirrai, kuma yana janyo ciwon daji da cutar da ke hana yara girma.
Sinadarin ya dade yana cutar da Afirka, har yakan janyo mutuwar dubban mutane da dabbobi.
Sinadarin fungi ne ke haddasa gubar Aflatoxin, wadda ke shafar tsirrai kamar masara da alkama da gyada, da sauran abubuwa irinsu madara da kwai daga dabbobin da aka ciyar da abincin da ya gurbata da gubar.
A kasashen da suka ci gaba, ana gwaji kan hatsin da ke zuwa kasuwa don tantance ko yana dauke da gubar Aflatoxin.
Amma a yankuna da yawa na kasashe masu tasowa, abincin da ya gurbata da gubar yakan kai har kwanon abincin mutane, sakamakon ba a yin gwaji, kuma kananan manoma sun dogara ne kan amfanin gonarsu don ciyar da iyalansu.
Barazanar gubar Aflatoxin ba wata sabuwar aba ba ce, hatta a Turai. Alal misali, a shekarun 1950-1960, dabbobi masu yawa sun mutu a Burtaniya sakamakon cin gyada da aka shigo da ita daga Kudancin Amurka.
A shekarar 2005, kasar Kenya ta sanar da mutuwar kimanin mutum 125, yayin da a 2016 Tanzania ta sanar da mutuwar mutane 14, duka sakamakon gubar Aflatoxin.
A cewar cibiyar bincike ta International Food Research Institute (IFPRI), kimanin ‘yan Afirka 26,000 ne suke mutuwa saboda cutar kansar hanta duk shekara, sakamakon mu’amala da gubar Aflatoxin.
Bayanai daga shirin Tanzania na Kiyaye Gurbatar Aflatoxin (TANIPAC), sun nuna cewa matsalar Aflatoxin na samuwa ne sakamakon rashin bin dokokin aikin noma, kama daga matakin noma, girbi, da ajiyar hatsi.
Ga yadda za a rage ko ma a kawar da gubar Aflatoxin daga abinci
TANIPAC tana bayar da shawarar sauya abin shuka a gona, da sauya nau’in tsirrai don taimakawa wajen rage yawan sinadarin toxin mai samuwa daga fungi - amfani da irin wanda ke iya jurewa harin fungi din da take janyo Aflatoxin.
Dole a bar kwantenonin da ake amfani da su wajen adana kayan hatsi su bushe sosai.
Hakanan, kayayyakin aikin gona da aka yi amfani da su wajen girbi su zama ba su da laima.
Masu bincike kuma sun yi gargadi kan kauracewa girbin amfanin gona kafin su gama nuna.
"A shekarar 2005, kasar Kenya ta sanar da mutuwar kimanin mutum 125, yayin da a 2016 Tanzania ta sanar da mutuwar mutane 14, duka sakamakon gubar Aflatoxin."
Amma sun ba da shawarar cewa ya fi kyau a yi girbi da wuri, sannan a busar da su da inji, bayan sun nuna.
Wannan zai rage hadarin fungi su hari amfanin gona.
Mataki na gaba shi ne a tsaftace hatsi a kuma cire kwanso da kuma hatsin da ya lalace, saboda yawanci suna dauke da sinadarin toxin mai yawa.
A karshe, dole a busar da hatsi sosai, ko masara ce, ko gyada ko alkama. Idan a lokacin damina ne, dole a busar da hatsi a-kai-a-kai kafin zuba su a ma’ajiya.
Kwararru kan harkar noma sun ba da shawarar a ringa duba hatsi duk bayan makonni uku ko hudu.
Ba a iya ganin Aflatoxin da ido kuru-kuru ko a ji warinsa da hanci. Kafin yin amfani da hatsi, a tsaftace shi sau biyu ko uku, don cire toxins da kuma maganin da aka yi amfani da shi lokacin ajiya.
Kwararru kan kiwon lafiya sun yi gargadi kan bai wa dabbobi kalen hatsin da aka tsafatce daga gubar, ko ruwan da aka wanke hatsin da ya gurbata da Aflatoxin.
Kauracewa zuba hatsi a kan tantagaryar kasa, saboda zai iya saurin daukar laima, wanda zai janyo daukar Aflatoxin.