Daga nan ta yi kira ga masu ruwa da tsaki kan harkokin fitar da kayayyaki da su hada gwiwa da hukumar NAFDAC saboda ci gaban kasar da makomarta /Hoto: NAFDAC

Hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya (NAFDAC) ta ce kashi 70 cikin 100 na kayan abincin da kasar take kai wa kasashen ketare ba sa samun karbuwa, wanda hakan yake jawo asara ga 'yan kasuwa da kuma kasar.

Darakta Janar din Hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan yayin bikin kaddamar da wani ofishin hukumar a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Lagos a karshen mako.

Ta ce kayan Nijeriya ba sa samun karbuwa a wasu daga cikin kasashen nahiyar Turai da kuma kasar Amurka.

Farfesan ta ce hakan na faruwa ne saboda kayan da Nijeriya ke samarwa ba su kai ingancin da ake bukata ba kuma ba sa iya cike ka'idoji da sharuddan da aka gindaya a kasashen da ake kokarin shigar da su.

Har ila yau ta ce hukumar NAFDAC ta fara daukar matakai don shawo kan wadannan kalubalen ta hanyar hada gwiwa da hukumomin gwamnati da ke filayen jiragen sama da tashohin ruwa don tabbatar da ingancin kayayyakin da ake fitarwa, da kuma tabbatar da cewa sun cika ka'idojin kasashen da aka yi niyyar kai su kafin a kammala hada su da kuma fara jigiyar su.

"Ganin yawan kudin da ake bukata don jigilar kayayyakin. Wannan babbar asara ce ga wadanda suke samar da kayayyakin da kuma kasar," in ji ta.

Ta ce akwai bukatar gwamnati ta kara sanya ido kan kayayyakin da ake fitarwa waje musamman yadda ake kada su da gwajin su da kuma kara tabbatar da ingancin su saboda su rage fuskantar matsalar rashin karbuwa a ketare.

Daga nan ta yi kira ga masu ruwa da tsaki kan harkokin fitar da kayayyaki da su hada gwiwa da hukumar NAFDAC saboda ci gaban kasar da makomarta.

Bugu da kari shugabar NAFDAC din ta ce suna aiki tare da Hukumar 'yan sanda kasa da kasa da Hukumar bincike ta Amurka (FBI) saboda wasu marasa gaskiya da ke da ruwa da tsaki a harkar fitar da kayayyakin.

A karshe ta ce rashin karbuwar da kayayyakin ke fuskanta a kasashen ketare musamman a Turai da Amurka ya kusa zuwa karshe, idan aka karfafa aiki tsakanin hukumar NAFDAC da sauran hukumomin gwamnati a iyakokin kasar.

TRT Afrika da abokan hulda