Hukumomin Uganda suna bincike kan wani abinci da ake zaton gurbatacce ne bayan da dalibai 150 students were taken to hospital.
An ce daliban sun fara korafi ne na ciwon ciki bayan da suka ci abincin dare a ranar Laraba a Babbar makarantar Sakandare ta Nakanyonyi da ke gundumar Mukono a yankin tsakiyar Uganda.
An kwantar da daliban 150 a wani asibitin yankin, sai dai babu wanda ya rasa ransa kuma an ba su kulawar da ta dace, a cewar wani mai magana da yawun 'yan sanda a hirarsa da TRT Afrika.
Ya ce tuni an sallami wasu daga cikinsu. "Maganar da muke yanzu haka yara 10 ne kawai ba a sallama ba," ya ce.
"E an kwantar da dalibai sakamakon cin gurbataccen abinci. Amma an sallame su tun jiya Alhamis sai dai bayan sun koma gida sai ciwon ya sake tasowa inda aka sake garzayawa da wasu asibiti," ya kara da cewa.
Hukumomin sun ce sun dauki nau'in abincin da daliban suka ci don aiwatar da bincike a kansa amma mafi yawan daliban sun samu lafiya bayan sallamar su.
Ya ce har yanzu 'yan sanda na sa ido kan lamarin "inda aka ajiye motocin daukar marasa lafiya na asibiti a makarantar."
"Mun dauki samfur don yin bincike don gano cewa ko gurbataccen abinci ne ko kuma mai guba ne," a cewar Onyango.