Yaran biyu suna noma ne tare da iyayensu, kwatsam sai suka fara nuna alamun shakewa/ Hoto AA

Wasu yara biyu 'yan gida daya sun rasa rayukansu a wani yanayi mai ban al'ajabi da ya sanya rudani, yayin da suke aikin gona tare da iyayensu a kyauyen Bafemgha, da ke yankin Mbouda a lardin yammacin kasar Kamaru.

Kamfanin dillacin labarai mai zaman kansa na Kamaru, CNA ya bayyana cewa ana zargin yaran sun taba wani abu mai guba ne suka kuma ci abinci ba tare da wanke hannun ba a ranar Talata.

‘’Yaran biyu da muka samu sunayensu Diffo Longfo Kuete dan kimanin shekara 7 da Massap Mervane dan kimanin shekaru 4, suna noma ne tare da iyayensu, kwatsam sai suka fara nuna alamun shakewa,’’ in ji CNA.

Mahaifiyar yaran ta shaida wa CNA cewa ‘’binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa yaran sun taba iri na wata masarar da aka adana da sinadarai masu guba ne, daga baya kuma suka ci shinkafa ba tare da wanke hannun ba.’’

Ta kara da cewa ‘’Dukanmu abinci iri daya muka ci a gona, kuma shinkafa ce, da muke gonar yaran sun shaida mana cewa za su je girbar lemar kwadi wato Mushroom, bayan mun kammala shuka da cin abinci, daga nan kuma ban san abin da ya faru ba.’’

Sashen rundunar 'yan sanda ta Babadjou Gendarmerie ya tabbatar da faruwar lamarin.

A shekarar da ta gabata ma dai irin wannan lamarin ya taba faruwa a kauyen na Bafemgha inda wasu yara biyu suka mutu bayan sun hadiye wani abu mai kamar guba.

TRT Afrika da abokan hulda