Wani mutum da ke zaune a Arewa Maso Yammacin Kamaru ya bayyana yadda 'yan a-waren kasar suka kashe da kuma kona matarsa da 'ya'yansa a yayin wani hari da suka kai yankin.
A wani sabon rahoto da kungiyar kare hakin dan adam ta Amnesty International ta fitar ranar Litinin, ta ambato mutumin, wanda ke kauyen Mbokop-Tanyi yana bayyana mata yadda lamarin ya faru.
Rahoton kungiyar, wanda ta tattara daga shekarar 2020 zuwa yanzu, ya bayyana mawuyacin halin da fararen-hula suka tsinci kansu a cikin a hannun 'yan a-waren da ke son kafa kasar Ambazonia da sojoji gwamnati da kuma 'yan sa-kai.
"Rahoton Amnesty International cikin tsanaki ya tattara jerin laifukan da 'yan a-ware masu dauke da makamai suka aikata kan fararen-hula, musamman a al'ummar Mbororo Fulani da ke Arewa maso Yamma.
Misali daya, a daren 28 ga watan Maris na 2022, 'yan a-ware dauke da makamai sun kai hari Mbororo Fulani da ke kauyen Mbokop-Tanyi. Amnesty International ta gana da wani magidanci wanda aka kashewa iyali uku.
Ya ce: “Yaran Amba [sunan da ake kiran masu rike da makamai] sun kona gidana da 'ya'yana biyu da matata a ciki. Sun harbe matata, kuma lokacin da ta fadi kasa, sun cinna mata wuta tare da 'ya'yana biyu mai shekara bakwai da dan wata shida, wadanda suke barci.”
Rahoton na Amnesty International ya ambato shugabar kungiyar a Yammaci da Tsakiyar Afirka, Samira Daoud tana yin kira "ga hukumomin Kamaru su binciki zarge-zargen keta hakkin dan adam da suka jibanci rikicin yankin da ake magana da turancin Ingilishi."
Kungiyar ta yi zargin cewa su ma masu rike da makamai na Mbororo Fulani da tallafin dakarun Kamaru sun kashe mutane tare da lalata wurare a yankin.
"Wata tawaga ta mutane masu rike da makamai da suka kai 45 wadanda aka bayyana a matsayin Fulani, Haoussa da Aku, da suka samu rakiyar sojojin Kamaru, sun kashe akalla mutane biyar tare da lalata gida 13 a kauyen Gheidze ranar 18 ga watan Oktoba na 2021," a cewar mutanen da Amnesty International ta ce ta tattauna da su.
Kungiyar ta yi kira ga kasashen da ke bai wa gwamnatin kasar makamai da su binciki yadda take amfani da su kafin su ci gaba da aika mata da su.