Iyalan wasu yara ‘yan kasar Gambiya 20 da suka mutu bayan sun sha maganin tari da wani kamfani daga kasar Indiya ya hada za su gurfanar da gwamnatinsu a gaban kotu a cikin wannan wata, bisa zarginsu da laifin rashin sa ido a safarar miyagun kwayoyi cikin kasar.
Wannan matakin dai ba kasafai ake daukar irinsa ba a daya daga cikin kasashen Afirka mafi fama da talauci, inda ‘yan kalilan mutane ke iya kalubalantar gwamnati.
Zarge-zargen da shaidu da iyayen suka bayar, wadanda kotu ta tattara su cikin takardu, da ta raba su ga kamfanin dillancin labarai na Reuters kawai, da ya ba da cikakken rahoto kan firgici da rudani gami da tashin hankali da magungunan suka haifar a kasar da tsarin kiwon lafiyarta ke tangal-tangal.
Takardun da iyalan suka bayar ya bayyana yadda suka shiga cikin damuwa ganin yadda 'ya'yansu suka mutu daga cututtuka da ba su kai su kashe su ba.
Wata uwa wacce ta bayyana cewa ta ci gaba da bai wa yaronta maganin mai dauke da guba har na tsawon kwana biyu cikin rashin sani sakamokon amai da ya fara yi, sai kuma wasu iyalai da suka ce an tilasta musu gyara ruwan dirip din da aka makala wa dansu a asibiti wanda aka ce yana kaucewa ba ya shiga yadda ya kamata.
A kalla yara 70 ne suka mutu sakamakon munanan raunukan da kodarsu ta samu a shekarar 2022, sanadin da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta danganta da wani maganin tari da kamfanin hada mugunguna da ke kasar Indiya mai suna Maiden Pharmaceuticals ya hada.
An dai zargi kamfanin da hada maganin mai guba da ke dauke da sinadarin diethylene glycol (DEG) da ethylene glycol (EG), sinadaran da aka saba amfani da su wajen hada gubar masana'antu da gubar da ke narkar da kankara.
A wasu lokutan a kan samu mutane marasa kishi da ke hada sinadaran DEG da EG saboda araharsu, a cewar wani masanin harhada magunguna.
A shekarar da ta gabata, an yi zargin wasu magungunan da aka hada su da sinadaran DEG da EG sun kashe kimanin yara 200 a Indonesia da Uzbekistan.
Biyan diyya
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito a baya, iyayen yara 20 daga cikin yaran sun dauki matakin doka a hannunsu, inda suke neman kusan dala 250,000 a matsayin diyya ga kowane yaro.
Lauyoyin Gambia uku sun ce wannan ita ce shari’a mafi girma da aka taba yi a kan ma’aikatar lafiya ta kasar da kuma hukumar kula da magunguna, da kuma shi kansa kamfanin na Maiden.
Al’amarin ya nuna irin hadarin da ke tattare da shigo da magunguna cikin kasashen da – kamar Gambia – ba su da hanyar gwada su kafin a sha.
Ya bayyana yadda a cikin yanayi na tattalin arzikin duniya ake iya gurbatattun magunguna da suke cutar da mutane ba tare da fayyace wata hanyar da za a iya bi don magance ko rage radadi ga wadanda abin ya shafa ba.
An sanya ranar 17 ga watan Yuli ne a matsayin ranar da za a fara sauraren karar, sannan sai a daga zaman zuwa tsawon kwana 30 don bai wa wadanda ake kara damar gabatar da martaninsu, in ji mai magana da yawun kotun.
Shari'ar da lauyoyin da suka shirya aiki ba tare da an biya su kudi ba, sun ce hukumomi a kasar sun gaza kiyaye dokokin da suka bukaci a tabbatar da cewa duk wasu magunguna da ake shigowa da su Gambia suna da inganci.
Wadanda ya kamata su sa ido "ba su dauki wani mataki wajen duba ko gwada ingancin maganin tarin ba kuma hakan ya saba wa ka’idoji na doka," a cewar takardar karar.
Kazalika takardar ta kara da cewa ma'aikatar lafiya ta gaza tabbatar da bin matakan ba da magunguna kafin a sha da kuma “tsarin kulawa da ake bukata.”
Ma'aikatar lafiya ta Gambia ba ta amsa bukatar yin tsokaci kan batun ba.
A cikin wata wasika da ta aike wa lauyoyin iyayen a watan Yuni, wadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani, ta ce an fara daukar matakai da dama, ciki har da bincike kan lamarin, wanda a halin yanzu ake ci gaba da nazari a kai.
Bayan mutuwar yaran, Babban Bankin Duniya ya amince da bai wa Gambia kudade don gina dakin gwajin magunguna.
Ana ci gaba da aikin tantance wurin da za a ajiye dakin, daga nan sai a fara ginin, a cewar wani mai magana da yawun gwamnati a watan da ya gabata.
Wasu abubuwan da za a lura da su
Kudaden da ake kashewa kiwon lafiyar a Gambia shi ne na uku mafi karanci a ma’aunin da Bankin Duniya ya bukaci kowace kasa ta dauka, inda aka ware dala 18.58 ga kowane mutum a shekarar 2020, kamar yadda bayanan bankin suka nuna.
Shaidar da iyayen suka bayar ta nuna rashin karfin tsarin da ake da shi wajen ba da taimako a lokacin da lamarin ya faru.
Cikin kusan rabin takardu 20 da iyayen suka gabatar sun ce sun samu jinkiri wajen samun kulawar gaggawa daga wajen likita ko kuma rashin gano wace cuta ce ke damun ‘yanyansu yayin da suke ta amai, suka kuma daina fitsari da rashin ci abinci bayan shan magungunan, a cewar wani sharhi da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi kan shaidar.
Wani iyali da aka zanta da shi ya ce rashin iskar oxygen ya sa aka jinkirta lura da dansu, wani kuma ya ce dole aka sa su gyara ruwan da aka makalawa dansu da ke diga.
Na uku kuma sun ce an sallami yaronsu daga asibiti duk da rashin yin fitsarin da ba ya iya yi na tsawon wasu kwanaki.
Biyar daga cikin iyayen sun kai ‘ya’yansu makwabciyar kasar Senegal saboda suna ganin za a fi samun wasu damammaki a can. Sai dai duk yara 20 da aka tafi da su sun mutu cikin ‘yan kwanaki da fara shan maganin.
Amie Jammeh, wata uwa da ta dauki danta mai shekara biyu, Mafugi Jassey zuwa wani kantin sayar da magani a tsakiyar watan Agusta lokacin da ya kamu da zazzabi, a takardar shaidar da ta bayar ta ce wani likitan ne ya hada mata wasu magunguna ta bai wa danta.
Daga nan ne ma'aikatar lafiya ta Gambiya ta aika da samfuran ruwan maganin na Maiden zuwa kasar waje don gwaji. Ba ta samu amsar sakamakon ba sai a watan Satumba.
Sa’a biyu bayan shan maganin kashi na farko, Mafugi ya fara amai. Mahaifiyarsa ta ci gaba da ba shi magungunan har tsawon kwana biyu.
Da Mafugi bai samu sauki ba, Jammeh ta kai shi asibiti inda ta lura da cewa ya daina yin fitsari. Bayan kwanciyar da suka yi a asibiti, sai da ta yi jiran kwana uku kafin likita ya zo ya duba su, a cewarta.
Zuwan likitan ke da wuya, Mafugi yana numfashi sama-sama, cikinsa da gabobinsa duk sun kumbura. Likitan ya ce Mafugi zai bukaci tiyata amma ana bukatar a yi gwajin jini domin sanin nau'in jinin yaron.
Yayin da suke cikin jiran gwaje-gwajen, Mafugi ya ce ga garinku nan a bayan mahaifiyarsa.