Ana ci gaba da bincike don gano daga ina maganin ya zo.  Hoto: Rueters

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa wani maganin tari na ruwa mai suna 'Naturcold' da ake sayar wa a Kamaru na dauke da sinadaran guba.

Wannan ne gargadi na baya-bayan nan game da yawan gurbatattun magungunan tari na ruwa da ake samu a kasar.

A ranar Larabar nan WHO ta sanar da cewa takardar bayanan da ke jikin kwalbar maganin na nuni da wani kamfani da ake kira Fraken International na kasar Ingila ne ya samar da maganin, amma kuma hukumar sanya idanu kan magunguna ta Ingila ta ce babu wani kamfani mai wannan suna a kasar.

"Ana ci gaba da bincike don gano daga ina maganin ya zo," in ji WHO.

Kakakin hukumar ya shaida wa Rueters cewa akwai yiwuwar ana ci gaba da sayar da maganin na ruwa a wasu shagunan Kamaru, wanda hakan ya sanya yin kira da a sanya idanu sosai.

A 2022, sama da yara 300 - mafi yawan su 'yan kasa da shekara biyar sun rasa rayukansu a Gambia da Indonesia da Uzbekistan sakamakon mummunan ciwon koda da shan irin wannan magani da wasu kamfanoni suka samar ya janyo musu.

Hukumar ta WHO ta kara da cewa wannan barazana na ci gaba har yanzu.

Mutuwar yara shida

An farga ne a Kamaru bayan da hukumar kula da amfani da magunguna ta kasar ta ce tana binciken mutuwar wasu yara shida da aka ba su maganin Naturcold.

WHO ta bayyana wa Rueters cewa tana kokarin taimaka wa mahukuntan kasar ne.

Adadin diethylene glycol, gurbataccen sinadarin da aka gano a cikin Naturcold ya haura kashi 28.6, wanda bai kamata ya wuce kashi 0.1 ba, in ji WHO.

A wasu lokuta marasa kishi na musanya sinadarin Propylene glycol, sinadarin da ake amfani da shi a magungunan ruwa, da wasu sinadaran masu rahusa irin su ethylene glycol da diethylene glycol, kamar yadda kwararru kan hada magunguna da dama suka shaida wa Rueters.

Gurbatattun sinadaran na iya janyo ciwon ciki da amai da gudawa da illata kodar mutum sosai, tare da sauran matsaloli da ka iya kai wa ga halaka dan adam.

Reuters