Hukumar da ke kula da kafofin watsa labarai ta kasar Kamaru, Conseil National de la Communication CNC, ta dakatar da wasu kafafen watsa labarai hudu na tsawon wata guda zuwa wata uku kan zarginsu da watsa kalamai na kiyayya a lokacin shirye-shiryensu.
Kamfanin dillancin labarai na Kamaru ya ruwaito cewa shugaban hukumar Joseph Chebongkeng ne ya sanar da hakan a wani zama da hukumar ta yi.
Baya ga kafafen watsa labaran da aka dakatar akwai wasu ‘yan jarida da aka dakatar.
Hukumar ta ce akwai gidan rediyon ‘Voice radio’ wanda aka dakatar na tsawon wata guda kan wasu kalamai na cin mutunci da aka yi wa wasu a lokacin wani shiri mai suna “ la republic armarge” a ranakun 9 da 22 ga watan Mayun 2023.
Hakazalika hukumar ta kuma dakatar da ma’aikacin Vision 4 TV wato Bruno Bidjang na tsawon wata guda sakamakon gaza nuna kwarewar aikin jarida yayin gudanar da shiri a ranar 16 ga watan Afrilun 2023.
Kamfanin dillancin labarai na Kamaru ya kuma ruwaito cewa manajan gidan talabijin na Info Tv shi ma an ba shi takardar gargadi.
Kasar Kamaru ita ce ta 138 a duniya ta bangaren ‘yanci da walwalar ‘yan jarida, kamar yadda kungiyar Reporters without boarders, RSF ta wallafa a shafinta.
Kungiyar ta RSF ta ce ‘yan jarida biyu aka kashe a bana a kasar sa’annan aka kama uku.