Rahotanni daga Kamaru na cewa 'yan a-waren kasar sun sace ma'aikatan gine-gine da dama a wurin da ake gina dakin binciken kimiyya a Arewa maso Yammacin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Cameroon News Agency ya rawaito cewa an sace ma'aikatan ne a makarantar Government Bilingual High School (GBHS) a garin Ndop.
Ndop shi ne gari mafi yawan jama'a a lardin Ngoketundjia da ke Arewa Maso Yammacin Kamaru.
Rahotanni sun ce satar mutanen, wadanda ya zuwa yanzu ba a san adadinsu ba, ta sa aiki ya tsaya cak a wurin.
Majalisar dokokin yankin Arewa maso Yammacin kasar ce ta dauki nauyin gina dakin binciken kimiyya na makarantar GBHS.
An yi garkuwa da ma'aikatan ne a ranar da gwamnan Arewa maso Yammacin kasar ya gargadi 'yan a-waren, sannan ya bukace su ajiye makamansu.
Rikici ya fara ne tsakanin yankin Arewa maso Yamma da kuma Kudu maso Yamma a shekarar 2016, inda malaman makaranta da lauyoyi suka kalubalanci kakaba musu magana da tsarin Faransanci.
A tsawon shekara shida na rikicin, fiye da mutum 6,000 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 600,000 suka kauracewa muhallinsu, a cewar bayanai.