Hukumomi sun ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da zakulo masu laifi a Jihar Kaduna don samar da tsaro da zaman lafiya.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna a raewacin Nijeriya ta kama mutum 503 da take zarginsu da aikata miyagun laifuka da suka hada da fashi da satar dabbobi da satar mutane da kisan kai da kwacen wayoyi da sauran laifuka.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Muhammed Jalige ya tabbatar wa da TRT Afirka cewa an yi nasarar wadannan kame ne tun daga satin farko na watan Mayu zuwa watan Yunin 2023.

Jalige ya ce korafe-korafen da suka yi ta samu daga wajen al’umma kan yawaitar kwacen wayoyi da jakar hannun mata ne da sauran laifuka suka sa rundunar kaddamar da samame a wuraren da ake tsammanin maboyar masu laifukan ne.

“Hakan ya sa muka kadamar da gagaruman jerin samame a watan Afrilu inda muka samu gagarumar nasara.

“Mun samu nasara a wadannan samame inda a tashin farko muka yi nasarar kama mutum 392 bisa zargin su da kwacen waya,” in ji jami’in ‘yan sandan.

A ranar Talatar da ta gabata ne rundunar ‘yan sandan ta ce ta gabatar da mutanen a hedikwatarta a Kaduna, sannan tuni ta gurfanar da su a gaban kotu don daukar matakan da suka dace a kansu.

Abubuwan da aka kwato

DSP Jalige ya ce an samu bindiga hudu samfurin AK47, da kananan bindiga ribolba uku da manyan bindigogi biyu da takalman ma’aikatan hukumar sufurin jiragen kasa 2,8000 da kuma motoci.

Kazalika rundunar ‘yan sandan ta ce ta kwato harsasai na AK47 har 129 da kuma tumaki.

Sannan a cikin wadanda aka kama din har da wani mutum Ismail Mohammed dan kauyen Maijere a karamar hukumar Lere, wanda ya taba sace dan uwansa sannan daga baya ya kashe shi bayan karbar kudin fansa har naira 120,000 daga iyalansa.

Jalige ya tabbatar da cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da zakulo masu laifi a Jihar Kaduna don samar da tsaro da zaman lafiya.

TRT Afrika