Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta sanar da nasarar kama mutum 52 da ake zargi da kwacen waya a hannun jama’a.
Rundunar ta sanar da hakan ne a wata sanarwa bayan kammala taron manema labarai da Kwamishin ‘yan sanda na jihar, Mohammed Usaini Gumel, ya yi a ranar Talata.
Kwamishinan ya bayyana nasarorin da rundunar ta samu cikin kwana 12 da suka wuce.
Wannan kame na zuwa ne a daidai lokacin da Jihar Kano ta dauki dumi kan yadda kwacen waya ke ta’azzara, lamarin da ke jawo asarar rayuka da jikkata, inda masu kwacen kan yi amfani da makamai don kwace wayoyin jama'a, wani lokacin lamarin kan kai ga yin ajalinsu.
CP Usaini Gumel ya ce ‘yan sanda sun yi nasarar kama mutum 96 a kwanaki 12, wadanda ake zargin su da aikata laifuka daban-daban kamar shan miyagun kwayoyi "da ake zaton shi ke tunzura su aikata laifuka" irin su kwacen waya da satar mutane don neman kudin fansa da fashi da makami da kuma satar ababen hawa da sauran wasu laifukan.
Kwacen waya
- Rundunar ta ce an samu laifuka na kwacen waya 18
- An kama mutum 52 da ake zargi da kwacen waya
- An kwato waya 71 daga hannun wadanda ake zargi da fashinsu
- An kwato makamai 150 daga hannun wadanda ake zargi da kwacen waya.
Miyagun kwayoyi
- An samu laifuka bakwai na tu’ammali da miyagun kwayoyi
- An kama mutum shida da ake zargi da hannu a tu’ammali da miyagun kwayoyi
- An kwace katan 20 na maganin tari na ruwa na Kodin
- An kwace kunshin kwaya 45
- An kwace kunshin wiwi 303
- An kwace kwayoyin Exol
- An kwace kwalbar maganin Diazepam 30
- Da kunshin sukudaye 30
Sauran manyan laifuka da suka faru
- An samu rahotannin faruwar wasu miyagun laifuka 25
- An kama mutum 38 da ake zargin su da aikata laifukan
- An kwace bindiga kirar gida uku da wasu muggan makaman kirar gida
- An kwato mota hudu da Keke Napep biyu da babur shida
- An samu allon alamar da ake sakawa kabari 28
- Da Jarkar manja biyu da iya kwandishan daya da tulun gas da fanka ta tsaye da agogunan hannu da talabijin ta zamani biyu da sauran su.
Rundunar ‘yan sandan ta ce ta samu wadannan nasarori ne a kokarinta na tabbatar da cewa an yi bikin mika mulkin gwamna lafiya lau a Jihar Kanon ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Sannan ta yi alkawarin ci gaba da aiki tukuru don wanzar da zaman lafiya da tsaro a jihar, karkashin hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
“Za mu ci gaba da kai samame da hada kai da sauran hukumomi don samun bayanan sirri da neman goyon bayan kafofin watsa labarai don wayar da kai a rediyo da talabijin da shafukan sada zumunta don samun nasara,” a cewar kwamishinan ‘yan sandan.
An shafe mako guda ana tafka muhawara a shafukan sada zumunta da ma duk wani wajen taruwar jama’a a Jihar Kano, kan batun kwacen waya, inda har aka dinga wallafa hotunan wadanda suka taba rasa rayukansu a wannan mummunar ta'asa.